+ -

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا: أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ أَحَدَكُمْ إِذَا مَاتَ عُرِضَ عَلَيْهِ مَقْعَدُهُ بِالْغَدَاةِ وَالعَشِيِّ، إِنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ الجَنَّةِ فَمِنْ أَهْلِ الجَنَّةِ، وَإِنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ النَّارِ فَمِنْ أَهْلِ النَّارِ، فَيُقَالُ: هَذَا مَقْعَدُكَ حَتَّى يَبْعَثَكَ اللَّهُ يَوْمَ القِيَامَةِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1379]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Lallai cewa idan ɗayanku ya mutu za’a bijiro masa da mazauninsa safiya da maraice, idan ya kasance daga cikin 'yan aljanna ne to yana daga cikin 'yan aljanna, idan ya kasance daga cikin 'yan wuta to yana daga cikin 'yan wuta, sai a ce: Wannan mazauninka ne har sai Allah Ya tasheka ranar alƙiyama".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1379]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa bawa idan ya mutu za'a bijiro masa da masaukinsa da gurinsa na musamman a cikin aljanna ko wuta, a farkon yini da ƙarshensa; wurinsa a aljanna idan ya kasance daga cikin 'yan aljanna, da kuma wurinsa a wuta idan ya kasance daga cikin 'yan wuta ne, kuma za’a ce masa: Wadannan wuraran ne wadanda za'a tasheka zuwa gare su ranar alƙiyama; a cikin hakan akwai ni'imtarwa ga mumini, da kuma azabtarwa ga kafiri.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Azabar ƙabari da ni'imarsa gaskiya ne.
  2. Ibnu Hajar ya ce: Lallai wannan bijirowar ga mumini mai tsoron Allah da kuma kafiri zahiri ne, amma mumini wanda ya cakuɗa ayyukansa sai a ɗauka akan cewa za'a bijiro masa da mazauninsa na aljannar da zai tafi zuwa gareta.
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Asami الهولندية الغوجاراتية الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin