Karkasawa: Aqida . Imani da Ranar Lahira .

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَمَّا خَلَقَ اللَّهُ الْجَنَّةَ وَالنَّارَ أَرْسَلَ جِبْرِيلَ عَلَيْهِ السَّلَامُ إِلَى الْجَنَّةِ، فَقَالَ: انْظُرْ إِلَيْهَا وَإِلَى مَا أَعْدَدْتُ لِأَهْلِهَا فِيهَا. فَنَظَرَ إِلَيْهَا فَرَجَعَ، فَقَالَ: وَعِزَّتِكَ لَا يَسْمَعُ بِهَا أَحَدٌ إِلَّا دَخَلَهَا. فَأَمَرَ بِهَا فَحُفَّتْ بِالْمَكَارِهِ، فَقَالَ: اذْهَبْ إِلَيْهَا فَانْظُرْ إِلَيْهَا وَإِلَى مَا أَعْدَدْتُ لِأَهْلِهَا فِيهَا. فَنَظَرَ إِلَيْهَا، فَإِذَا هِيَ قَدْ حُفَّتْ بِالْمَكَارِهِ، فَقَالَ: وَعِزَّتِكَ لَقَدْ خَشِيتُ أَنْ لَا يَدْخُلَهَا أَحَدٌ. قَالَ: اذْهَبْ فَانْظُرْ إِلَى النَّارِ وَإِلَى مَا أَعْدَدْتُ لِأَهْلِهَا فِيهَا. فَنَظَرَ إِلَيْهَا فَإِذَا هِيَ يَرْكَبُ بَعْضُهَا بَعْضًا، فَرَجَعَ فَقَالَ: وَعِزَّتِكَ لَا يَدْخُلُهَا أَحَدٌ. فَأَمَرَ بِهَا فَحُفَّتْ بِالشَّهَوَاتِ، فَقَالَ: ارْجِعْ فَانْظُرْ إِلَيْهَا. فَنَظَرَ إِلَيْهَا فَإِذَا هِيَ قَدْ حُفَّتْ بِالشَّهَوَاتِ، فَرَجَعَ وَقَالَ: وَعِزَّتِكَ لَقَدْ خَشِيتُ أَنْ لَا يَنْجُوَ مِنْهَا أَحَدٌ إِلَّا دَخَلَهَا».

[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce :
"Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi - zuwa Aljanna, sai ya ce: ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta sai ya dawo, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa wani daya ba zai ji ta ba sai ya shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan ki, sai Ya ce; Tafi zuwa gareta ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga ta an kewayeta da abubuwan ki, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa shiga cikinta . Ya ce: Tafi ka yi duba zuwaga wuta da kuma abinda na tanada ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga shashininta yana hawa kan sashi, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa ba wanda zai shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan sha'awa , sai ya ce; ka koma ka yi duba zuwa gareta, sai ya yi duba zuwa gareta sai ga shi ita kuma an kewayeta da abubuwan sha’awa, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa tsira daga gareta a ce bai shigeta".

Hasan ne - Abu Daud Ya Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa lokacin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, ya cewa (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -: Ka tafi zuwa ga Aljanna ka duba ta, sai ya tafi ya kallace ta sosai sannan ya dawo, Sai (Malaika) Jibril ya ce: Eh, ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa ba wanda zai ji labarin ta da kuma abinda ke cikinta na ni'ima da girmamawa da alkarai sai ya so ya shigeta, kuma ya yi aiki saboda ita. Sannan Allah Ya kewaye Aljanna da abubuwan ki da wahalhalu na aikata umarni da kuma nisantar abubuwan da aka hana; to ya wajaba ga wanda yake son shigarta da ya ketare wadananan abubuwan kin. Sannan Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Ya Jibril! ka tafi ka duba Aljanna, bayan ya kewayeta da abubuwan ki, Sai ya tafi ya dubata, sannan ya zo sai ya ce: Eh, ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa ina jin tsoro da kada wani ya kasa shigarta saboda wahalhalu da tsananin da suke akan hanyarta. Lokacin da Allah Ya halicci wuta, sai ya ce; Ya Jibri! ka tafi ka kallaceta, sai ya tafi ya kallaceta. Sannan ya zo sai (Malaika) Jibril ya ce: Eh ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa babu wani da zai ji labarin azabarta da tashin hankalin cikinta, sai ya ki shigarta ya nisanta daga sabubban shigarta. Sannan Allah - mai girma da daukaka - Ya kewaye wuta, Ya sanya hanya zuwa gareta da sha'awowi da abubuwan jin dadi, sannan Ya ce: Ya Jibril, ka tafi ka yi duba zuwa gareta, Sai (Malaika) Jibril ya tafi sai ya yi duba zuwa gareta, sannan ya dawo sai ya ce: Ya Ubangiji, na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoro na ji tausayin kada wani ya kasa tsira daga gareta; saboda abinda ke gefanta na sha'awowi da abubuwan jin dadi.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Imani da cewa Aljanna da wuta suna nan a yanzu haka.
  2. Wajabcin yin imani da abinda ke boye da kuma dukkanin abinda ya zo daga Allah da manzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. Muhimmancin hakuri akan abubuwan ki; domin su ne hanya masu kaiwa zuwa ga Aljanna.
  4. Muhimmancin nisantar abubuwan da aka haramta; domin su ne hanya mai kaiwa zuwa ga wuta.
  5. Sanya Aljanna abar kewayewa da abubuwan ki, wuta kuma da sha'awowi, shi ne ke hukunta jarraba a rayuwar duniya.
  6. Hanyar Aljanna mai wahala ce, kuma tana bukatuwa zuwa ga hakuri da fama tare da imani, hanyar wuta kuma abin cikawa ce da abubuwan jin dadi da sha'awowwi a anan duniya.