عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«يُؤْتَى بِالْمَوْتِ كَهَيْئَةِ كَبْشٍ أَمْلَحَ، فَيُنَادِي مُنَادٍ: يَا أَهْلَ الجَنَّةِ، فَيَشْرَئِبُّونَ وَيَنْظُرُونَ، فَيَقُولُ: هَلْ تَعْرِفُونَ هَذَا؟ فَيَقُولُونَ: نَعَمْ، هَذَا المَوْتُ، وَكُلُّهُمْ قَدْ رَآهُ، ثُمَّ يُنَادِي: يَا أَهْلَ النَّارِ، فَيَشْرَئِبُّونَ وَيَنْظُرُونَ، فَيَقُولُ: وهَلْ تَعْرِفُونَ هَذَا؟ فَيَقُولُونَ: نَعَمْ، هَذَا المَوْتُ، وَكُلُّهُمْ قَدْ رَآهُ، فَيُذْبَحُ ثُمَّ يَقُولُ: يَا أَهْلَ الجَنَّةِ خُلُودٌ فَلاَ مَوْتَ، وَيَا أَهْلَ النَّارِ خُلُودٌ فَلاَ مَوْتَ، ثُمَّ قَرَأَ: {وَأَنْذِرْهُمْ يَوْمَ الحَسْرَةِ إِذْ قُضِيَ الأَمْرُ وَهُمْ فِي غَفْلَةٍ} [مريم: 39]، وَهَؤُلاَءِ فِي غَفْلَةٍ أَهْلُ الدُّنْيَا {وَهُمْ لاَ يُؤْمِنُونَ} [مريم: 39]».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4730]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki, sai mai kira ya yi kira: Yaku 'yan Aljanna, sai su dago kawunansu suna dubawa, sai ya ce: Shin kun san wannan? sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, dukkaninsu kuma sun ganta, sannan ya yi kira: Yaku 'yan wuta, sai su miko kawunansu suna dubawa, sai ya ce: Shin kun san wannan? sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu sun ganta, sai a yankata sannan ya ce: Ya ku 'yan Aljanna dawwama babu mutuwa, ya ku 'yan wuta dawwama babu mutuwa, sannan ya karanta: {Kuma ka yi musu gargadin ranar nadama yayin da aka hukunta al'amari alhali su suna cikin rafkana} [Maryam: 39], wadannan suna cikin rafkanannun mutane a duniya {Su ba su Imani ba} [Maryam: 39]".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4730]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa Za’a zo da mutuwa ranar Alkiyama, kamar siffar namijin tinkiya a jikinsa akwai fari da baki, Sai a yi kira: Ya ku 'yan Aljanna! sai su dago wuyan su da kawunansu suna dubawa. Sai ya ce da su: Shin kun san wannan?. Sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu hakika sun ganta sun kuma santa, Sannan mai kira ya yi kira: Ya ku 'yan wuta, sai su dago wuyansu su dago kawunansu suna dubawa. Sai ya ce: Shin kun san wannan?. Sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu hakika sun gan ta. Sai a yankata, sannan mai kira ya ce: Ya ku 'yan Aljanna wanzuwa har abada babu mutuwa,m. Ya ku 'yan wuta wanzuwa har abada babu mutuwa. Wannan dan ya zama kari a cikin ni'imar muminai, da masifa a cikin azabar kafirai. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta: {Kuma ka yi musu gargadi da ranar nadama a lokacin da aka hukunta al’amari alhalin kuwa suna a cikin rafkana, kuma ba su yin imani ba.} Ranar Alkiyama za'a rabe tsakanin 'yan Aljanna da 'yan wuta, kuma kowanne zai shiga inda zai dawwama a cikinsa. Sai mai munanawa ya yi nadama dan bai kyautata ba, mai takaitawa kuma dan bai kara alheri ba.