Karkasawa: Aqida . Imani da Ranar Lahira .

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«نَارُكُمْ جُزْءٌ مِنْ سَبْعِينَ جُزْءًا مِنْ نَارِ جَهَنَّمَ»، قِيلَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنْ كَانَتْ لَكَافِيَةً. قَالَ: «فُضِّلَتْ عَلَيْهِنَّ بِتِسْعَةٍ وَسِتِّينَ جُزْءًا كُلُّهُنَّ مِثْلُ حَرِّهَا».

[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wutarku wani yankine daga yanki saba'in daga wutar Jahannama", (Sai) aka ce: Ya Manzon Allah, ta kasance ta isa (dan azabtarwa), ya ce: "An fifita ta a kansu da yanki sittin da tara, kowannen su tamkar zafinta yake”.

Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wutar duniya wani yanki ne daga yanki saba'in daga wutar Jahannama, Wutar lahira karfin zafinta yana karuwa akan zafin wutar duniya da yanki sittin da tara, kowanne yanki daga gareta yana daidai da zafin wutar duniya. Sai aka ce : Ya Manzon Allah lallai cewa wutar duniya ta isa dan azabtar da masu shigarta. Sai ya ce: An fifita wutar Jahannama akan wutar duniya da yanki sittin da tara, kuma dukkaninsu tamkarta ne a cikin tsananin zafi.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Gargadarwa daga wuta dan mutane su nisanci ayyukan da zasu kai su zuwa gareta.
  2. Girman wutar Jahannama da azabarta, da kuma tsananin zafinta.