عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: "مَنْ لَقِيَ الله لا يُشْرِك به شَيئا دخل الجنَّة، ومن لَقِيَه يُشرك به شيئا دخَل النار".
[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...
Daga Jabir Dan Abdullahi zuwa ga Annabi:"Duk Wanda ya gamu da Allah baiyi masa shirka ba to zai shiga Aljanna, kuma duk wanda ya gamu da shi alhalin yana yi Masa shirka to zai shiga Wut"
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi]
Annabi yana bamu labari a cikin wannan Hadisin cewa lallai Duk wanda ya Mutu baiyi shirka da Allah ba da komai a cikin Rubibiyya sa ne ko a cikin Uluhiyya sa ne ko kuma a cikin sunayensa ne ko sifofinsa to zai shiga Aljanna, kuma idan ya Mutu Mushiriki to makomarsa ita ce wuta.