+ -

عن عدي بن حاتم رضي الله عنه : "أنه سمع النبي صلى الله عليه وسلم يقرأ هذه الآية: "اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ وَالْمَسِيحَ ابْنَ مَرْيَمَ وَمَا أُمِرُوا إِلاَّ لِيَعْبُدُوا إِلَهًا وَاحِدًا لا إِلَهَ إِلاَّ هُوَ سُبْحَانَهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ" فقلت له: إنا لسنا نعبدهم، قال: أليس يُحَرِّمُونَ ما أحل الله فتُحَرِّمُونَهُ؟ ويُحِلُّونَ ما حَرَّمَ الله فتُحِلُّونَهُ؟ فقلت: بلى، قال: فتلك عبادتهم".
[صحيح] - [رواه الترمذي]
المزيــد ...

An samo daga Adi Dan Hatim -Allah ya yarda dashi- "cewa ya ji Annabi -tsira da amincin Allah yana karanta wannan ayar: Sun riki malamansu "yahudawa" da malamansu "nasarawa" abin yiwa bauta ba Allah ba haka nan Isa Dan Maryam. kuma ba'a umarce su ba sai da cewa su bautawa abin bauta shi kadai wanda ba abin bautawa da cancanta sai shi tsarki ya tabbatar masa game da abin da suke yi masa tarayya? sai na ce da shi: lallai mu ba bauta musu muke yi ba. sai ya ce: shin ba haramta abin da Allah ya halatta suke ba sai ku ma ku haramta shi? kuma su halarta abin da Allah ya haramta ku ma ku halarta shi ba? sai nace: ey.Sai yace wannan ita ce bauta musu din."
Ingantacce ne - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi

Bayani

yayin da wannan Sahabin mai girma yaji karatun Manzon Allah-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-na wannan ayar wacce ta kunshi labarin yahudu da nasara:cewa sun mayar da malamansu da masu ibadar cikinsu abin bauta,suna shar'anta musu abinda yasabawa shari'ar Allah kuma suyi musu biyayya a kan haka,to sai ma'anar ayar ta rikitar,domin shi sahabin ya zaci cewa bauta ta takaita akan yin sujjada da makamantanta,sai Manzo -tsira da amincin Allah-ya bayyana masa cewa yana daga bautawa malamai yi musu biyayya a wajan haramta halal da kuma halarta haram,sabanin hukunci Allah madaukaki da Manzonsa tsira da aminci su tabbata a gare shi

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci
Manufofin Fassarorin