عن ابن مسعود رضي الله عنه قال: "جاء حَبْرٌ من الأحبار إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم فقال: يا محمد، إنا نجد أن الله يجعل السماوات على إِصْبَعٍ، والأَرَضَينَ على إِصْبَعٍ، والشجر على إِصْبَعٍ، والماء على إِصْبَعٍ، والثَّرَى على إِصْبَعٍ، وسائر الخلق على إِصْبَعٍ، فيقول: أنا الملك، فضحك النبي صلى الله عليه وسلم حتى بَدَتْ نَوَاجِذَهُ تَصْدِيقًا لقول الحبر، ثم قرأ: (وَمَا قَدَرُوا اللَّهَ حَقَّ قَدْرِهِ وَالأَرْضُ جَمِيعًا قَبْضَتُهُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ). وفي رواية لمسلم: "والجبال والشجر على إِصْبَعٍ، ثم يَهُزُّهُنَّ فيقول: أنا الملك، أنا الله". وفي رواية للبخاري: "يجعل السماوات على إِصْبَعٍ، والماء والثَّرَى على إِصْبَعٍ، وسائر الخلق على إِصْبَعٍ".
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

An karbo daga Dan Mas'ud Allah ya yarda dashi yace:"Wani Malami daga Malaman Yahudawa yazo wajan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai yace:Ya Muhammad,hakika mun samu cewa Allah zai sanya Sammai akan yatsa,kuma kassai akan Yatsa,kuma Bishiyu akan Yatsa,kuma Ruwa akan Yatsa,kuma Kasa akan Yatsa,kuma sauran Halittu akan Yatsa,sannan yace:Nine Mamallaki.Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi Dariya har Fikokinsa suka bayyana saboda gasgata fadin Malamin Yahudawan.Sannan ya karanta:Kuma basu kaddara Allah akan Hakikanin ikon yinsa ba kuma Kasa duka damkarsace a Ranar Kiyama?.Acikin wata Riwaya ta Muslim:"Da Duwatsu da Bishiyu akan Yatsa,sannan ya girgizasu sannan yace:Nine Mamallaki,nine Allah".Kuma acikin wata Riwaya ta Bukhari:"Zai sanya Sammai akan Yatsa,kuma Ruwa da Kasa akan Yatsa,kuma sauran Halitta akan Yatsa"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Dan Mas'ud-Allah ya yarda dashi-yana bamu labari cewa wani Mutum daga Malaman Yahudawa yazo wajan Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-ya ambata masa cewa sun samu cikin Littattafansu cewa Allah -tsarkakekken Sarki-Ranar Al-kiyama zai sanya Sammai a Yatsa,kuma kassai a Yatsa,kuma Bishiyu a Yatsa,kuma Kasa aYatsa,.Awata Riwayar:kuma Ruwa akan Yatsa,kuma sauran ababan Halitta akan Yatsa,dagaYatsunsa-Mai-Girma da Daukaka-,kuma ita Biyarce kamar yadda yazo acikin Riwayoyi ingantattu,kuma ba kamar Yatsun ababan Halitta bace,kuma cewa shi zai bayyana wani abu daga Ikonsa da Girmansa Mai-Girma da Daukaka sannan sai ya girgizasu kuma ya bayyana Mulkinsa na Hakika,da cikar tasarrufinsa saki ba kaidi da Uluhiyyarsa ta Gaskiya.Sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi Dariya har Fikokinsa suka bayyana saboda gasgata fadin Malamin Yahudawan,sannan ya karanta:{Kuma basu kaddara Allah akan Hakikanin ikon yinsa ba Kasa duka damkarsa ce a Ranar Kiyama}.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Kurdawa
Manufofin Fassarorin
Kari