عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم:
«اللهُمَّ لَا تَجْعَلْ قَبْرِي وَثَنًا، لَعَنَ اللهُ قَوْمًا اتَّخَذُوا قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ».
[صحيح] - [رواه أحمد] - [مسند أحمد: 7358]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ya Allah kada Ka maida kabarina gunki, Allah Ya la'anci mutanen da suka maida kaburburan Annabawansu masallatai".
[Ingantacce ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [مسند أحمد - 7358]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya roki Ubangijinsa da kada Ya maida kabarinsa tamkar gunkin da mutane suke bauta masa ta hanyar girmama shi, da fuskantarsa a cikin sujjada, sannan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sanar da cewa Allah Ya nisantar Ya kore wanda ya maida kaburburan Annabawa masallatai daga rahamarsa' domin maida su masallatai sila ce zuwa bauta musu da kuma kudircewa a cikinsu.