عن ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما أنه سَمِعَ رَجُلًا يَقُولُ: لَا وَالْكَعْبَةِ، فَقَالَ ابْنُ عُمَرَ: لَا يُحْلَفُ بِغَيْرِ اللَّهِ، فَإِنِّي سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«مَنْ حَلَفَ بِغَيْرِ اللهِ فَقَدْ كَفَرَ أَوْ أَشْرَكَ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي وأحمد] - [سنن الترمذي: 1535]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji wani mutum yana cewa: A'a na rantse da Ka'abah, sai Dan Umar ya ce: Ba'a rantsuwa da wanin Allah, domin cewa ni na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka".
[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 1535]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labarin cewa wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah da sunayensa da siffofinsa to hakika ya kafircewa Allah ko ya yi shirka; domin rantsuwa tana hukunta girmama wanda aka rantse da shi, girma kadai ya tabbata ga Allah ne Shi kadai; ba'a rantsuwa sai da Allah da sunayensa da siffofinsa - tsarki ya tabbatar masa, Wannan rantsuwar tana daga karamar shirka; saidai da a ce mai rantsuwa ya girmama abinda ya rantse da shi kamar girmama Allah - Madaukakin sarki - ko sama da haka; to a wannan lokacin zai zama daga babbar shirka.