+ -

عَن عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمِنين رضي الله عنها زَوْجَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حَدَّثَتْهُ قَالَتْ:
جَاءَتْنِي امْرَأَةٌ مَعَهَا ابْنَتَانِ تَسْأَلُنِي، فَلَمْ تَجِدْ عِنْدِي غَيْرَ تَمْرَةٍ وَاحِدَةٍ، فَأَعْطَيْتُهَا فَقَسَمَتْهَا بَيْنَ ابْنَتَيْهَا، ثُمَّ قَامَتْ فَخَرَجَتْ، فَدَخَلَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَحَدَّثْتُهُ، فَقَالَ: «مَنْ يَلِي مِنْ هَذِهِ البَنَاتِ شَيْئًا، فَأَحْسَنَ إِلَيْهِنَّ، كُنَّ لَهُ سِتْرًا مِنَ النَّارِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5995]
المزيــد ...

Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta ce:
Wata mata ta zo a tare da ita akwai 'ya'yanta biyu mata, bata samu komai awurina ba banda wani dabino ɗaya, sai na bata shi sai ta raba shi tsakanin 'ya'yan nata mata biyu, sannan ta tashi sai ta fita, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo sai ta zantar da shi, sai ya ce: «‌Wanda ya jiɓinci wani abu daga waɗannan 'ya'ya matan, sai ya kyautata musu, zasu zama kariya gare shi daga wuta».

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5995]

Bayani

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa wata mata ta zo mata a tare da ita akwai 'ya'yanta biyu mata tana tambayarta ta bata abinda zata ci, Nana A'isha bata samu komai a wurinta ba banda dabino ɗaya, sai ta bata shi sai matar ta raba dabinon tsakanin 'ya'yan nata mata biyu ba ta ci komai daga gare shi ba, sannan ta tashi sai ta fita, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga (gida) sai Nana A'isha ta zantar da shi, sai ya ce: Duk wanda ya jiɓinci wani abu daga waɗanan 'ya'ya matan, sai ya kyauata musu ya tarbiyantar da su ya ciyar da su ya shayar da su ya tufatar da su kuma ya yi haƙuri akan haka, zasu zama sutura da kariya gare shi daga wuta.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kula da 'ya'ya mata da kuma ƙoƙari garesu yana daga cikin mafificin ayyukan alheri masu nisantarwa daga wuta.
  2. An so yin sadaka da abinda mutum yake da iko a kansa koda ya zama kaɗan ne.
  3. Tsananin tausayin iyaye ga 'ya'yayensu.
  4. Bayanin halin ɗakunan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma cewa arziƙinsa ya zama tsakatsakiya ne (ya ishe shi).
  5. Bayanin falalar fifita wani akan kai kuma cewa hakan yana daga cikin alamomin muminani; haƙiƙa Nana A'isha - Allah Yarda da ita - ta fifita waccan matar da 'ya'yanta biyu akan kanta, wannan yana nuni akan kyautarta da kuma karamcinta tare da tsananin buƙatuwarta.
  6. An ambaci kyautar 'ya'ya mata da jarraba; saboda abinda ke cikin renonsu na wahala da gajiya, ko saboda wasu mutane suna ƙin su, ko domin cewa yana rinjaya cewa basu da wata hanya ta samun kuɗi da kuma rayuwa.
  7. Musulunci ya zo yana mai tunɓuke al'adun Jahiliyya munana, daga cikin hakan shi ya yi wasicci da 'ya'ya mata.
  8. (Mutum) zai iya samun wannan ladan ko da ta kasance 'ya ɗaya ce kamar yadda ya zo a cikin wasu daga cikin ruwayoyi.
Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Swahili Yaran Tailand Asami الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin