عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«إِنَّ الْمُقْسِطِينَ عِنْدَ اللهِ عَلَى مَنَابِرَ مِنْ نُورٍ، عَنْ يَمِينِ الرَّحْمَنِ عَزَّ وَجَلَّ، وَكِلْتَا يَدَيْهِ يَمِينٌ، الَّذِينَ يَعْدِلُونَ فِي حُكْمِهِمْ وَأَهْلِيهِمْ وَمَا وَلُوا».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1827]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Lallai masu adalci a wurin Allah suna kan munbarirrika na haske, a daman Ubangiji Al-Rahman - Mai girma da ɗaukaka - su duka hannayensa biyun na dama ne, waɗanda suke adalci a hukuncinsu da iyalansu da abin da suka jiɓinta".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1827]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa waɗanda suke hukunci da adalci da gaskiya a tsakanin mutane waɗanda suke ƙarƙashin shugabancinsu da hukuncinsu da iyalansu, cewa su za su zauna a kan abubuwan zama maɗaukaka haƙiƙa an haliccesu daga haske, don girmamawa garesu a ranar al-ƙiyama. Waɗannan munbarorin suna daman Ubangiji Al-Rahman, kuma su duka hannayensa biyun na dama ne.