عَنْ أَبِي حَازِمٍ قَالَ: قَاعَدْتُ أَبَا هُرَيْرَةَ رضي الله عنه خَمْسَ سِنِينَ، فَسَمِعْتُهُ يُحَدِّثُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ:
«كَانَتْ بَنُو إِسْرَائِيلَ تَسُوسُهُمُ الأَنْبِيَاءُ، كُلَّمَا هَلَكَ نَبِيٌّ خَلَفَهُ نَبِيٌّ، وَإِنَّهُ لاَ نَبِيَّ بَعْدِي، وَسَيَكُونُ خُلَفَاءُ فَيَكْثُرُونَ» قَالُوا: فَمَا تَأْمُرُنَا؟ قَالَ: «فُوا بِبَيْعَةِ الأَوَّلِ فَالأَوَّلِ، أَعْطُوهُمْ حَقَّهُمْ، فَإِنَّ اللَّهَ سَائِلُهُمْ عَمَّا اسْتَرْعَاهُمْ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3455]
المزيــد ...
Daga Abu Hazim ya ce: Na zauna da Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - shekara biyar, sai na ji shi yana zantarwa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce;
"Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantarsu, duk lokacin da wani Annabi ya rasu sai wani Annabin ya maye gurbinsa, lallai cewa babu wani Annabi a baya na, za'a samu halifofi zasu yawaita" Suka ce: Da me zaka umarce mu? ya ce: "Ku cika caffar na farko sai na farko, ku basu haƙƙinsu, domin cewa Allah Mai tambayarsu ne daga abinda Ya basu kiwo".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3455]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantar su, suna jiɓintar al'amuransu kamar yadda sarakuna da shugabanni suke aikatawa da talakawansu, a duk lokacin da ɓarna ta bayyana a cikinsu sai Allah Ya aiko musu da wani Annabin da zai daidaita al'amarinsu kuma ya gusar da abinda suka canja na hukunce-hukunce. Lallai cewa babu wani Annabi a bayana (ballantana) ya aikata abinda waɗancan suke aikatawa, za'a samu halifofi a bayana zasu yawaita kuma jayayya da saɓani zasu faru a tsakaninsu. Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Da me zaka umarce mu? Sai ya ce: Idan Aka yi wa halifa caffa bayan wani halifan; to caffar na farko ce ingantacciya wajibine a cikata, caffar na biyun kuma ɓatacciya ce kuma nemanta yana haramta, kuma ku basu haƙƙinsu, ku bisu ku yi mu'amala da su da ji da bi inba a saɓon ba ne, domin cewa Allah Zai tambayesu kuma Zai yi musu hisabi a kan abinda suke aikata shi gareku.