عَنْ أَبِي بَكْرٍ الصِّدِّيقَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
نَظَرْتُ إِلَى أَقْدَامِ الْمُشْرِكِينَ عَلَى رُءُوسِنَا وَنَحْنُ فِي الْغَارِ، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ لَوْ أَنَّ أَحَدَهُمْ نَظَرَ إِلَى قَدَمَيْهِ أَبْصَرَنَا تَحْتَ قَدَمَيْهِ، فَقَالَ: «يَا أَبَا بَكْرٍ، مَا ظَنُّكَ بِاثْنَيْنِ اللهُ ثَالِثُهُمَا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2381]
المزيــد ...
Daga Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na kalli digadigan mushrikai akan kawunanmu alhali mu muna cikin kogo, sai na ce: Ya Manzon Allah da a ce ɗayansu zai kalii digadigansa zai ganmu a ƙarƙashin digadigansa, sai ya ce: «Ya Abubakar, me kake zato da mutum biyun da Allah Shi ne na ukunsu».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2381]
Sarkin muminai Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - a lokacin hijira: Na kalli digadigan mushrikai alhali su suna tsaye akan kawunanmu a saman kogon Hira alhali mu muna cikinsa, sai na ce: Ya Manzon Allah da a ce ɗayansu zai yi duba zuwa ga digadigansa zai ganmu ƙarƙashin digadigansa, sai ya ce : Ya Abubakar, me kake zato da mutum biyu Allah ne na ukunsu da nasara da kuma taimako, da kiyayewa da kuma daidaita?!