عَنْ مُعَاذَةَ قَالَتْ:
سَأَلْتُ عَائِشَةَ، فَقُلْتُ: مَا بَالُ الْحَائِضِ تَقْضِي الصَّوْمَ، وَلَا تَقْضِي الصَّلَاةَ؟ فَقَالَتْ: أَحَرُورِيَّةٌ أَنْتِ؟ قُلْتُ: لَسْتُ بِحَرُورِيَّةٍ، وَلَكِنِّي أَسْأَلُ. قَالَتْ: كَانَ يُصِيبُنَا ذَلِكَ، فَنُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّوْمِ، وَلَا نُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّلَاةِ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 335]
المزيــد ...
Daga Mu'azah ta ce :
Na tambayi Nana A'isha, sai na ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah? Sai ta ce: Shin ke baharuriyyace? na ce: Ni ba baharuriyya ba ce, sai dai tambaya nake. Ta ce: Hakan yana samunmu, sai a umarcemu da rama azimi, ba'a umartarmu da rama sallah.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 335]
Mu'azah al'adawiyya - ta tambayi uwar muminai Nana A'isha - Allah Yarda da ita -, sai ta ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah? Sai ta ce mata: Shin ke daga Khawarijawa Hirarura’a kike ne ? waɗanda suke yawaita tambaya dan ta'annuti da kuma tsanantawa? Na ce: Ni ba baharuriyyababa ce, sai dai tambaya nake yi, ta ce: al’ada tana samunmu tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai a umarcemu da rama azimi, ba'a umartarmu da rama sallah.