عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤمنين رضي الله عنها أَنَّ فَاطِمَةَ بِنْتَ أَبِي حُبَيْشٍ سَأَلَتِ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَتْ:
إِنِّي أُسْتَحَاضُ فَلاَ أَطْهُرُ، أَفَأَدَعُ الصَّلاَةَ؟ فَقَالَ: «لَا، إِنَّ ذَلِكِ عِرْقٌ، وَلَكِنْ دَعِي الصَّلاَةَ قَدْرَ الأَيَّامِ الَّتِي كُنْتِ تَحِيضِينَ فِيهَا، ثُمَّ اغْتَسِلِي وَصَلِّي».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 325]
المزيــد ...
Daga A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Fatima 'yar Abu Hubaishi ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce :
Ni ina yin jinin cuta bana tsarkaka, shin zan bar sallah ne? sai ya ce: "A'a, Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi Sallah.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 325]
Fadima 'yar Hubaishin ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Lallai ni jini ba ya yanke mini, yana zarcewa har a lokacin da ba na al’ada ba, shin hukuncin hakan zai zama hukuncin al’ada sai inbar sallah? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mata: Lallai shi jinin cuta ne, shi jinin rashin lafiya ne yana faruwa daga yankewar jijiya a mahaifa, ba jinin haila ba ne, Idan lokacin haila ya zo wanda kika kasance kina haila a cikinsa akan al'adarki ta wata kafin ki yi rashin lafiya da jinin cuta, to ki bar sallah da azimi da wasunsu , na abinda haila take hanawa a lokacin al’ada . Idan gwargwadan lokacin ya kare sai ki zama kin yi tsrki, to sai ki wanke gurin jinin, sannan ki wanke jikinki cikakken wankewa dan dauke hadasi, sannan ki yi sallah.