عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضي الله عنها أَنَّهَا قَالَتْ:
إِنَّ أُمَّ حَبِيبَةَ بِنْتَ جَحْشٍ الَّتِي كَانَتْ تَحْتَ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ عَوْفٍ شَكَتْ إِلَى رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم الدَّمَ، فَقَالَ لَهَا: «امْكُثِي قَدْرَ مَا كَانَتْ تَحْبِسُكِ حَيْضَتُكِ، ثُمَّ اغْتَسِلِي». فَكَانَتْ تَغْتَسِلُ عِنْدَ كُلِّ صَلَاةٍ.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 334]
المزيــد ...
Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Cewa Ummu Habiba 'yar Jahsh wacce take ƙarƙashin Abdurrahman Dan Awf ta kawo koken (zubar) jini ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce mata: "Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sannan ki yi wanka". Ta kasance tana wanka a kowacce sallah.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 334]
Daya daga cikin sahabbai mata ta kawo koken zubar jini (jinin Istihara) zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da take fama da shi, sai ya umarceta ta dakatar da sallah gwargwadan abinda hailarta take tsareta kafin zuubar wannan al'amarin da ya faru da ita, sannan ta yi wanka ta yi sallah, ta kasance tana wanka dan neman lada a kowacce sallah.