+ -

عن أُمِّ عَطِيَّةَ رَضي الله عنها، وكَانَتْ بايَعَت النبيَّ صلى الله عليه وسلم، قالت:
كُنَّا لا نَعُدّ الكُدرَةَ والصُّفْرَةَ بعدَ الطُّهرِ شيئًا.

[صحيح] - [رواه أبو داود بهذا اللفظ، ورواه البخاري بدون زيادة (بعد الطهر)] - [سنن أبي داود: 307]
المزيــد ...

Daga Ummu Adiyya - Allah Ya yarda da ita -, ta kasance ta yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - caffa, ta ce:
Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fatsi a bakin komai bayan tsarki.

[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 307]

Bayani

Sahabiyya Ummu Adiyya - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa mata a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sa daukar ruwan da yake fita daga farji - wanda launinsa yake karkata zuwa baƙi, ko fatsi-fatsi - bayan ganin tsarki cewa yana daga al’ada, saboda haka ba sa barin sallah ko azimi saboda shi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ruwan da yake zuba daga farjin mace - bayan tsarkaka daga al’ada - ba'a izina da shi koda a tare da shi akwai launin hanta-hanta da fatsi-fatsi wanda ya samu ta hanyar jini.
  2. Zubar hanta-hanta da fatsi-fatsi a lokacin al’ada da al'ada ana daukarsa a matsayin al’ada; Domin cewa shi jini ne a lokacinsa, sai dai mai cakuduwa ne da ruwa.
  3. Mace ba ta barin sallah ko azimi saboda hanta-hanta da fatsi-fatsi wanda yake a bayan tsarki, kawai ta yi alwala ta yi sallah.