عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ: خَرَجَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي أَضْحَى أَوْ فِطْرٍ إِلَى المُصَلَّى، فَمَرَّ عَلَى النِّسَاءِ، فَقَالَ:
«يَا مَعْشَرَ النِّسَاءِ، تَصَدَّقْنَ، فَإِنِّي أُرِيتُكُنَّ أَكْثَرَ أَهْلِ النَّارِ» فَقُلْنَ: وَبِمَ يَا رَسُولَ اللَّهِ؟ قَالَ: «تُكْثِرْنَ اللَّعْنَ، وَتَكْفُرْنَ العَشِيرَ، مَا رَأَيْتُ مِنْ نَاقِصَاتِ عَقْلٍ وَدِينٍ أَذْهَبَ لِلُبِّ الرَّجُلِ الحَازِمِ مِنْ إِحْدَاكُنَّ»، قُلْنَ: وَمَا نُقْصَانُ دِينِنَا وَعَقْلِنَا يَا رَسُولَ اللَّهِ؟ قَالَ: «أَلَيْسَ شَهَادَةُ المَرْأَةِ مِثْلَ نِصْفِ شَهَادَةِ الرَّجُلِ» قُلْنَ: بَلَى، قَالَ: «فَذَلِكِ مِنْ نُقْصَانِ عَقْلِهَا، أَلَيْسَ إِذَا حَاضَتْ لَمْ تُصَلِّ وَلَمْ تَصُمْ» قُلْنَ: بَلَى، قَالَ: «فَذَلِكِ مِنْ نُقْصَانِ دِينِهَا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 304]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'ida Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita zuwa wurin da ake sallah, a babbar sallah ko a ƙarama, sai ya wuce inda mata suke, sai ya ce:
"Yaku wannan mata, ku yi sadaka, dan ni an nuna min cewa kune mafi yawan 'yan wuta". Sai suka ce: Dan me ya Manzon Allah? ya ce: "Kuna yawaita tsinuwa, kuma kuna butulcewa zamantakewa, banga masu tawayar hankali da Addini mafi tafiyar da hankalin namiji ba mai karfin niyya kamar ɗayanku ba", suka ce: To menene tawayar Addininmu da hankalinmu ya Manzon Allah? ya ce: "Shin yanzu bai zama cewa shaidar mace kwatankwacin rabin shaidar namiji ba ce" suka ce: Eh, ya ce: "To wannan yana daga tawayar hankalinta, shin yanzu idan ta yi al’ada ba ta sallah ba ta azimi" suka ce: Eh, ya ce: "To wannan yana daga tawayar Addininta".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 304]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita a ranar idi zuwa wurin sallah, ya kasance haƙiƙa ya yi wa mata alƙawarin cewa zai waresu da wa'azi, sai ya zartar da shi a wannan ranar, kuma ya ce: Yaku wannan jama'a ta mata ku yi sadaka, kuma ku yawaita istigfari; su suna daga mafi girman sabubban kawar da kurakurai, domin cewa ni na ganku a daren Isra'i mafi yawan 'yan wuta.
Sai wata mace daga cikinsu mai hankali da tunani da nutsuwa ta ce: Meke damu ya Manzon Allah (mune) mafi yawancin 'yan wuta?
Ya ce: Dan wasu al'amuara: Kuna yawaita tsinuwa da zagi, kuma kuna musun haƙƙin miji. Sannan ya siffanta su da faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ban ga masu tawayar hankali da Addini ba mafi rinjaye ga ma'abocin tinani da hankali da karfin niyya da kiyayewa ga al'amari ba kamar ku.
Ta ce: Ya Manzon Allah, menene tawayar hankali da Addini?
Ya ce: Amma tawayar hankali to shaidar mace biyu ta yi daidai da shaidar namiji ɗaya; to wannan tawayar hankali ne, tawayar Addini ita ce tawayar aiki na gari inda zata zauna wasu darere da kwanuka ba ta sallah saboda al’ada, kuma tana ajiye azimi wasu kwanuka saboda al’ada, to wannan tawayar Addini ne, sai dai cewa su ba'a zarginsu akan hakan kuma ba'a kamasu akan su ; domin cewa shi yana daga asalin halitta, kamar yadda mutum an ɗabi'antar da shi kuma an halicce shi yana son dukiya kuma mai gaggawa a al'amuransa kuma mai jahilci...da wanin haka, sai dai ya faɗakar akan hakan dan gargaɗarwa daga fitinuwa da su.