kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

"Wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, kuma Annabi Isa bawan Allah ne kuma ManzonSa ne kalmarSa ne da ya jefa ta ga nana Maryamu kuma Ruhi ne daga gare Shi, kuma aljanna gaskiya ce haka wuta ma gaskiya ce, @Allah Zai shigar da shi Aljanna akan aikin da yake akansa".
عربي Turanci urdu
"Wanda ya gamu da Allah ba ya tarayya da shi da wani to zai shiga Aljanna, wanda kuma ya gamu da shi yana shirka da shi to zai shiga wuta".
عربي Turanci urdu
"Duk wanda ya lamunce min abinda ke tsakanin mukamukansa biyu da abinda ke tsakanin kafafuwansa biyu zan lamunce masa aljanna".
عربي Turanci urdu
"Aljanna ita ce mafi kusa daga dayanku daga igiyar takalminsa, wuta ma tamkar hakan".
عربي Turanci urdu
"An kewaye wuta da sha'awowi, kuma an kewaye Aljanna da abubuwa ki".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi* - zuwa Aljanna, sai ya ce: ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta sai ya dawo, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa wani daya ba zai ji ta ba sai ya shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan ki, sai Ya ce; Tafi zuwa gareta ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga ta an kewayeta da abubuwan ki, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa shiga cikinta . Ya ce: Tafi ka yi duba zuwaga wuta da kuma abinda na tanada ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga shashininta yana hawa kan sashi, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa ba wanda zai shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan sha'awa , sai ya ce; ka koma ka yi duba zuwa gareta, sai ya yi duba zuwa gareta sai ga shi ita kuma an kewayeta da abubuwan sha’awa, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa tsira daga gareta a ce bai shigeta".
عربي Turanci urdu
"Za’a zo da mutum ranar Alkiyama, sai a jefa shi a cikin wuta, sai hanjin cikinsa su fita, sai ya kewaya da su kamar yadda jaki yake kewaye da dutsen nika*, sai 'yan wuta su taru gare shi, sai su ce: Ya wane me ya sameka? shin baka kasance kana umarni da aikin alheri ba, kuma kana hani daga abin ki? sai ya ce: Eh, hakika na kasance ina horo da aikin alheri amma bana aikata shi, kuma ina hani daga abin ki (mummuna) kuma ina aikata shi".
عربي Turanci urdu
Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yayin da ya ji wata kara, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin kun san mene ne wannan?" ya ce: Muka ce: Allah da ManzonSa ne mafi sani, ya ce: @"Wannan wani dutsene da aka jefa shi cikin wuta tun shekara saba'in, shi (dutsan) yana faɗawa cikin wuta a yanzu, har sai da ya kai karshanta".
عربي Turanci urdu
Na kasance tare da Sa'eed bin Jubair sai ya ce: Wanene a cikinku ya ga duniyar da ta share jiya? Na ce: Ni ne, sai na ce: Amma ni ba na cikin sallah, amma an yi min duri
عربي Turanci urdu
Akwai matakai guda dari a Sama wanda Allah ya tanadar wa mujahidai a tafarkin Allah, tsakanin darajoji biyu kamar tsakanin sama da kasa
عربي Turanci urdu
Duk wanda ya auri mata biyu a tafarkin Allah muna so a kira shi daga kofofin sama, ya Abdullahi, wannan shi ne mafi alheri, saboda haka duk wanda yake cikin ma'abota sallah ana kiransa sallah, kuma duk wanda yake cikin masu jihadi ana kiran shi daga kofar jihadi
عربي Turanci urdu
"Lallai cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba wanda yake da takalma biyu da igiyoyi na wuta, ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa kamar yadda (tukunyar) tagulla take tafarfasa, ba ya ganin cewa wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi shi ne mafi sauƙin azabarsu"
عربي Turanci urdu
Shin ba zan gaya muku wanda aka hana wuta ba? Ko kuma wa ya haramta ta wuta? Haramtacce ne ga kowane dangi mai sauki ne, mai taushi kuma mai sauki
عربي Turanci urdu
Wasu daga cikinsu suna dauke wuta a kan dugadugansa, wasu kuma suna dauke shi zuwa gwiwowinsa, wasu kuma suna daukarsa
عربي Turanci urdu
Za a shigar da Jahannama a wannan rana a kansa saboda iyayengiji dubu saba'in, tare da kowace sarauta ta sarakuna dubu saba'in da suke jan ta
عربي Turanci urdu
"Mutane Uku ba zasu shiga Al-janna ba: Mashayin giya da mai yanke Zumunci, da Mai Gasgata Masu Sihiri"
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
: : : :
عربي Turanci urdu
: :
عربي Turanci urdu
Lallai 'yan Al-janna suna gano Xakunan waxanda suke samansu kamar yadda kuke ganin Tauraro mai haske da ya wuce a sararin sama daga Gabas ko kuma Yamma don fifikon da ke tsakaninsu
عربي Turanci urdu
Wallahi Kwarin bakar cikin Al-janna yafi Alkairi daga abunda rana ta futo mata ko ta faxar Mata (Wato Duniya)
عربي Turanci urdu
.
عربي Turanci urdu
. : :
عربي Turanci urdu
Shin kuna cutar ganin rana da tsakar rana, ba cikin gajimare ba? Suka ce: A'a. Ya ce: Shin kuna shan wahala wurin ganin wata a daren cikakken wata, ba cikin gajimare ba?
عربي Turanci urdu
"Za’a zo da mtuwa kamar siffar farin rago da sirkin baki*, sai mai kira ya yi kira: Yaku 'yan Aljanna, sai su dago kawunansu suna dubawa, sai ya ce: Shin kun san wannan? sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, dukkaninsu kuma sun ganta, sannan ya yi kira: Yaku 'yan wuta, sai su miko kawunansu suna dubawa, sai ya ce: Shin kun san wannan? sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu sun ganta, sai a yankata sannan ya ce: Ya ku 'yan Aljanna dawwama babu mutuwa, ya ku 'yan wuta dawwama babu mutuwa, sannan ya karanta: {Kuma ka yi musu gargadin ranar nadama yayin da aka hukunta al'amari alhali su suna cikin rafkana} [Maryam: 39], wadannan suna cikin rafkanannun mutane a duniya {Su ba su Imani ba} [Maryam: 39]".
عربي Turanci urdu
"Wutarku wani yankine daga yanki saba'in daga wutar Jahannama*", (Sai) aka ce: Ya Manzon Allah, ta kasance ta isa (dan azabtarwa), ya ce: "An fifita ta a kansu da yanki sittin da tara, kowannen su tamkar zafinta yake”.
عربي Turanci urdu
‘’Na tsinkaye a cikin Aljannah sai nag a mafiya yawan ahalinta talakawa ne ,Na leqa Wuta kuma sai nag a mafiya yawan ahalinta mata ne
عربي Turanci urdu
Al-janna da Wuta sunkai Qara, sai wuta ta ce: ni ta Masu jabberanci ce da Masu girman kai, ita kuma Al-janna Sai ta ce: ni ta Raunanan Mutane da Miskinan su ce
عربي Turanci urdu
Na tashi a ƙofar Sama, kuma idan mutum na kowa ya shiga ciki, ana jefa talakawa, da sahabban kakan-kakan
عربي Turanci urdu
Idan mumini ya san abin da Allah yake da shi na azaba, babu wanda zai yi kwadayin aljannarsa, kuma idan kafiri ya san abin da Allah ya yi na rahama, babu wanda zai karai daga aljannarsa
عربي Turanci urdu
Kwadaitarwa zuwa ga samun ni'imar Aljanna har abada, da tsoratarwa daga azabar wuta mai zafi
عربي Turanci urdu
"An bijiro min da aljanna da wuta ban ga kamar abinda na gani yau ba na alheri da sharri, da kun san abinda na sani da kun yi dariya kaɗan kuma kun yi kuka da yawa*" ya ce: Babu wani yini da ya taɓa zowa sahabban manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mafi tsanani kamar wannan yinin, ya ce: Sai suka rufe kawunansu suna ruri, ya ce: Sai Umar ya miƙe sai ya ce: Mun yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin annabi, ya ce: Sai wani mutum ya miƙe sai ya ce: Waye babana? ya ce: "Babanka shi ne wane", sai wannan ayar ta sauka: {Yaku waɗanda suka yi imani kada ku tambayi wasu abubuwa idan suka bayyana gareku zasu munana muku}. [al-Ma'ida: 101].
عربي Turanci urdu
Mu'ujizar Allah - Mai girma da daukaka - na mutanen da za su shiga Aljanna a cikin sarkoki
عربي Turanci urdu
Saihan da Jihan da Furat da Nil baki xayan su kogunan Al-janna ne
عربي Turanci urdu
Wuta da Aljanna sunyi Jayayya, sai wuta ta ce: an zaveni saboda masu girman kai, da Masu jiji da Kai, kuma Aljanna ta ce: Ni kuma babu mai shiga ta sai raunanan Mutane da waxanda ba komai ba, da wacanda idonsu bai buxe da Duniya ba
عربي Turanci urdu
Aljannatai guda biyu kwanikansu na Azurfa, da abunda yake cikinsu, da Kuma Aljannatai guda biyu kwanukansu na Zinariya, da abunda yake cikinsu, kuma abunda yake tsakanin Mutane da abunda yake tsakanin suga Ubangijinsu, babu komai sai wani Mayafi na xaukaka akan fuskarsa a cikin Aljannar Zama
عربي Turanci urdu
"Lallai a cikin aljanna akwai wata bishiya mahayin doki horarre mai sauri zai yi tafiyar shekara ɗari ba zai iya wuceta ba".
عربي Turanci urdu
"Lallai a cikin aljanna akwai wata kasuwar da 'yan aljanna suke zuwanta kowacce Jumu'a*, sai iskar arewa ta taso sai ta watsu a fuskokinsu da tufafinsu, sai su ƙara kyau da ƙawa. sai su koma zuwa ga iyalansu alhali haƙiƙa sun ƙara kyau da ado, sai iyalansu suce musu: Wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ƙawa a bayanmu, sai su ce: Kuma wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ado a bayanmu".
عربي Turanci urdu
Babu Wani Musulmi da 'Yayansa Uku zasu Rasu waxanda basu Balaga ba sai Allah ya shigar da shi Al-janna saboda falalar rahamarsa gare su
عربي Turanci urdu
Idam Ranar Al-kiyama ta Kasance Allah ai Tura ga kowane Musuli Bayahude daya Ko banasare, sai yace wannan zai kwanceka daga Wuta
عربي Turanci urdu
Dukkan abunda nabawa bawana halal ne, Kuma lallai ni na halicci bayi na kan turba baki xayan, kuma lallai su Shaixanu sun zo musu suka kautar da su daga Addinin su
عربي Turanci urdu
Al-janna da wuta sun kai kara, sai Aljanna ta ce: Raunana ne da miskinai zasu shige ni, Sai wuta ta ce: Ni kuma Jabberan Mutane da Masu girman kai ne za su shige ni, sai ya ce da Wuta: ke Azaba ta ce, kuma ina yin Ukuba da ke ga wanda na so, Kuma ya ce da Al-jannah: Ke Rahama ta ce, kuma ina jin kan wanda na su da ke
عربي Turanci urdu
"Lallai 'Yan Al-janna suna ganin Dakunan a cikin Al-Jannah kamar yadda kuke ganin Taurari a Sama"
عربي Turanci urdu
«Ya Abu Sa'id, wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin Addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin Annabi, aljanna ta wajaba a gare shi»*, sai Abu Sa'id ya yi mamaki gareta (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaitata mini ya Manzon Allah, sai ya maimaita, sannan ya ce: «Ɗayar kuwa za'a ɗaukakawa bawa daraja ɗari da ita a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja biyu kamar tsakanin sama da ƙasa ne». Ya ce: Waccece ya Manzon Allah? Ya ce: «Jihadi a tafarkin Allah, jihadi a tafarkin Allah».
عربي Turanci urdu
«Lallai mafi ƙankantar matsayin ɗayanku a cikin aljanna shi ne Ya ce masa: Ka yi buri, sai ya yi buri, kuma ya yi buri, sai Ya ce da shi: Shin ka yi burin kuwa? sai ya ce: Eh, sai Ya ce da shi: @Lallai kana da abin da ka yi burin da kwatankwacin sa tare da shi».
عربي Turanci urdu
"Lallai mumini yana da wata shema a cikin aljanna ta lu'ulu'u ɗaya mai ƙofa a cikinta, tsawonta mil sittin ne, mumini yana da mata a cikinta, mumini zai kewayesu amma sashinsu ba zai ga sashi ba".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
«Lallai cewa farkon jama'ar da zasu shiga aljanna akan surar wata daren goma sha huɗu, sannan masu biye musu akan surar tauraro mafi tsananin haske*, ba sa fitsari ba sa bahaya, ba sa tofar da yawu kuma ba sa tofar da majina, abin taje kansu shi ne zinare, kuma guminsu shi ne almiski, kuma abin kunna tiraren wutarsu shi ne icen tiraren wuta, kuma matansu sune Hurul inun (Masu tsananin farin ido da tsananin ƙwayar baƙin da ke cikin idon), suna a kan halittar mutum ɗaya, akan surar babansu (Annabi) Adam, zira'i sittin a cikin sama».
عربي Turanci Indonisiyanci