+ -

عَنْ أُسَامَةَ بْنِ زَيْدٍ رضي الله عنه قَالَ: قِيلَ لَهُ: أَلَا تَدْخُلُ عَلَى عُثْمَانَ فَتُكَلِّمَهُ؟ فَقَالَ: أَتَرَوْنَ أَنِّي لَا أُكَلِّمُهُ إِلَّا أُسْمِعُكُمْ؟ وَاللهِ لَقَدْ كَلَّمْتُهُ فِيمَا بَيْنِي وَبَيْنَهُ، مَا دُونَ أَنْ أَفْتَتِحَ أَمْرًا لَا أُحِبُّ أَنْ أَكُونَ أَوَّلَ مَنْ فَتَحَهُ، وَلَا أَقُولُ لِأَحَدٍ يَكُونُ عَلَيَّ أَمِيرًا: إِنَّهُ خَيْرُ النَّاسِ بَعْدَمَا سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«يُؤْتَى بِالرَّجُلِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ، فَيُلْقَى فِي النَّارِ، فَتَنْدَلِقُ أَقْتَابُ بَطْنِهِ، فَيَدُورُ بِهَا كَمَا يَدُورُ الْحِمَارُ بِالرَّحَى، فَيَجْتَمِعُ إِلَيْهِ أَهْلُ النَّارِ، فَيَقُولُونَ: يَا فُلَانُ مَا لَكَ؟ أَلَمْ تَكُنْ تَأْمُرُ بِالْمَعْرُوفِ، وَتَنْهَى عَنِ الْمُنْكَرِ؟ فَيَقُولُ: بَلَى، قَدْ كُنْتُ آمُرُ بِالْمَعْرُوفِ وَلَا آتِيهِ، وَأَنْهَى عَنِ الْمُنْكَرِ وَآتِيهِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2989]
المزيــد ...

Daga Usama ɗan Zaid - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An ce masa: Shin ba zaka shiga gurin Usman ba ka yi masa magana? sai ya ce: Shin kuna ganin cewa ni ba za yi masa magana ba har sai na fada muku? wallahi hakika na yi masa magana tsakanina da shi, ba tare da na buɗe kofar wani al'amarin da bana son in zama na farkon wanda zai buɗeshi ba, kuma ba zan cewa wani dan ya zama sarkina (shugabana) ba: Cewa shi ne mafi alherin mutane bayan na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Za’a zo da mutum ranar Alkiyama, sai a jefa shi a cikin wuta, sai hanjin cikinsa su fita, sai ya kewaya da su kamar yadda jaki yake kewaye da dutsen nika, sai 'yan wuta su taru gare shi, sai su ce: Ya wane me ya sameka? shin baka kasance kana umarni da aikin alheri ba, kuma kana hani daga abin ki? sai ya ce: Eh, hakika na kasance ina horo da aikin alheri amma bana aikata shi, kuma ina hani daga abin ki (mummuna) kuma ina aikata shi".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2989]

Bayani

An cewa Usama ɗan Zaid Allah - Ya yarda da su - Shin baka shiga wurin Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ba ka yi masa magana cikin abinda yake faruwa na fitina tsakanin mutane da kokari a kasheta gabaɗayanta, sai ya sananar da su cewa shi ya yi masa magana a sirri dan neman maslaha badan tada fitina ba, manufarsa cewa shi ba ya son bayyanar da inkari ga sarakuna a cikin jama'a, sai ya zama sababi na rena khalifa, kuma shi ne kofar fitina da sharri ba zan zama farkon wanda zai buɗeta ba.
Sannan Usama - Allah Ya yarda da su - ya ce: Shi yana yi wa sarakuna nasiha a boye kuma ba ya yi wa wani mujamala koda sarki ne, kuma ba ya yi musu fadanci sai ya yabe su a gabansu da karya, hakan bayan ya ji daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi za’a zo da wani mutum ranar alkiyama, sai a jefa shi a cikin wuta, sai hanjin (kayan) cikinsa su fito daga cikinsa da gaggawa saboda tsananin zafi da tsananin azaba, sai ya kewaya da 'ya'yan cikinsa yana wannan halin kamar kewayawar jaki a gefan dutsen nikansa, sai 'yan wuta su taru a gefansa kamar sarkar data kewaye shi, sai su tambaye shi : Ya wane, shin ba kaine ka kasance kana umartarmu da aikin alheri ba kuma kake hanamu abin ki ba?!
Sai ya ce: Lallai ni na kasance ina horo da aikin alheri amma bana aikata shi, kuma ina hani daga abin ki kuma ina aikata shi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الرومانية Malagasy
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Asali a cikin nasiha ga shugabanni ta kasance tsakaninsa da su ne, kuma kada mutum ya yaɗa abin a gaban gamagarin mutane.
  2. Narko mai tsanani na azaba ga wanda maganarsa ta sabawa aikinsa.
  3. Ladabi tare da sarakuna (shugabani) da tausasa musu, da umartarsu da aikin alheri, da kuma hanasu abin ki.
  4. Zargin yi wa shugabanni mujamala a kan gaskiya, da kuma bayyanar da abinda ya boye sabaninsa kamar mai fadanci da karya.