عن سهل بن سعد رضي الله عنه عن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«مَنْ يَضْمَنْ لِي مَا بَيْنَ لَحْيَيْهِ وَمَا بَيْنَ رِجْلَيْهِ أَضْمَنْ لَهُ الْجَنَّةَ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6474]
المزيــد ...
Daga Sahal Dan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Duk wanda ya lamunce min abinda ke tsakanin mukamukansa biyu da abinda ke tsakanin kafafuwansa biyu zan lamunce masa aljanna".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6474]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labari game da al'amura biyu idan musulmi ya lazimce su to cewa shi zai shiga aljanna,
Na farko: Kiyaye harshe daga maganar da zata fusatar da Allah - Madaukakin sarki -.
Na biyu: Kiyaye farji daga afkawa a cikin alfasha.
Domin cewa wadannan gabubuwa biyun afkawa cikin sabo da su yana yawaita.