+ -

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤمنينَ رضي الله عنها قَالَتْ:
كُنْتُ أَغْتَسِلُ أَنَا وَالنَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ إِنَاءٍ وَاحِدٍ كِلاَنَا جُنُبٌ، وَكَانَ يَأْمُرُنِي، فَأَتَّزِرُ، فَيُبَاشِرُنِي وَأَنَا حَائِضٌ، وَكَانَ يُخْرِجُ رَأْسَهُ إِلَيَّ وَهُوَ مُعْتَكِفٌ فَأَغْسِلُهُ وَأَنَا حَائِضٌ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 299]
المزيــد ...

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce :
Na kasance ina wanka ni da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga kwarya (abin wanka) daya mu duka biyun muna da janaba, ya kasance yana umartata, sai insa gwafso, sai ya rungumeni alhali ni ina al’ada, ya kasance yana fito min da kansa alhali shi yana i'itikafi sai in wanke masa shi alhali ina al’ada.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 299]

Bayani

Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari game da sashin halayenta na musamman tare da shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, daga hakan: Ta kasance tana wankan janaba tare da shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- daga kwarya daya sai su dinga diban ruwan tare. Kuma cewa shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi idan ya yi nufin zuwa mata alhali tana al’ada sai ya umarceta ta rufe jikinta daga cibiya zuwa gwiwa, sai ya rungumeta da abinda ke koma bayan jima'i. Kuma cewa shi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance yana i'itikafi a cikin masallaci sai ya fitar da kansa ga Nana A'isha alhali tana cikin dakinta tana al’ada.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Halaccin wankan mutum da matarsa a kwarya daya.
  2. Halaccin rungumar mai al’ada a abinda ke kasa da farji, kuma cewa jikinta mai tsarki ne.
  3. An so sanyawarta gwafso a lokacin rungumemeniya.
  4. Rikon sabubba masu hana afkawa cikin haram.
  5. Hana mai al’ada zama a cikin masallaci.
  6. Halaccin tabawarta abubuwa danyu da busassu, daga hakan (akwai) wanke gashi da tsefe shi.
  7. Kyakkyawan mu'amalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga iyalansa.