عن عائشة رضي الله عنها قالت: «كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يعجبه التيمُّن في تَنَعُّلِّه، وترجُّلِه، وطُهُورِه، وفي شَأنه كُلِّه».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga A'isah -Allah ya yarda da ita- tace:"Manzon Allah ya kasance Damantawa tana burge shi wajen sanya takalminsa,da taje kansa,da tsarkinsa,da sha'aninsa duka
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

A'isha Allah ya yarda da ita tana bamu labari game da al'adar Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi ita ce gabatar da dama ciki saha'anin sanya takalaminsa da taje kansa,da kuma tsarkinsa da kuma dukkanin al'amuransa wadanda aka ambata kamar sanya riga ko wando,kamar yin barci da ci dashi da makamantan haka.dukkan wannan saboda fata na gari da kuma fifita dama akan hagu.ammma bubuwa na kazanta mafi kyau a gabatar da hagu, don haka Annabi ya yi hana yin tsarki da hannun dama, ya kuma hana shafa gaba da hannun dama,domin shi hannun dama don kyawawan abubuwa ne,hagu kuma ga abin da yake ba haka ba.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili
Manufofin Fassarorin