عن البراء بن عازب رضي الله عنهما قال: «ما رأيتُ من ذِي لِمَّةٍ في حُلَّةٍ حَمْرَاءَ أحسنَ من رسول الله صلى الله عليه وسلم ، له شَعْرٌ يَضْرِبُ مَنْكِبَيْهِ، بعيدُ ما بين المَنْكِبَيْنِ، ليس بالقصير ولا بالطويل».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Barra'a Bn Azib -Allah ya yarda da su- ya ce: "Ban tava ganin wani mai gashin da ya sauko kafaxa ba cikin jajayan kaya yai kyau kamar Manzon Allah SAW ba, yana da gashi da ya sauka kan kafaxunsa, kuma mai faffaxan kafaxu, kuma ba Gajere ba kuma ba Dogo ba"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Barra'a Bn Azib -Allah ya yarda da su- ya Siffanta Manzon Allah SAW a cikin wannan Hadisin:: "Ban tava ganin wani mai gashin da ya sauko kafaxa ba cikin jajayan kaya yai kyau kamar Manzon Allah SAW ba, yana da gashi da ya sauka kan kafaxunsa, kuma mai faffaxan kafaxu, kuma ba Gajere ba kuma ba Dogo ba SAW