عن أبي هريرة رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم : «ما من مَكْلُومٍ يُكْلَمُ في سبيل الله، إلا جاء يومَ القيامة، وكَلْمُهُ يَدْمَى: اللَّونُ لَوْنُ الدَّمِ، والرِّيحُ رِيحُ المِسْكِ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ba wani wanda aka yi wa rauni a tafarkin Allah face sai ya zo Ranar Alkiyama, raunin nasa yana jini: kalarsa kalar jini, kanshinsa kuma kanshinalmiski
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Annabi tsira da amincin Allah yana bayyana mana falalar jihadi a tafarkin Allah Madaukaki da kuma irin abin da mai jihadi ke samu, na lada, cewa duk wanda aka yiwa rauni a tafarkin Allah ko an kashe shi ko ya warke, to zai zo Ranar kiyama gaban al'umma da damarar yaki, zai zo da ciwonsa danye, yana da launin jini kanshin Almiski.