عَنْ أَبِي عَبْسٍ عَبْدُ الرَّحْمَنِ بْنِ جَبْرٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَا اغْبَرَّتْ قَدَمَا عَبْدٍ فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَتَمَسَّهُ النَّارُ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 2811]
المزيــد ...
Daga Abu Abs Abdurrahman ɗan Jabr - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Diga-digan wani bawa ba su taɓa ƙura a cikin tafarkin Allah ba, kuma wuta ta shafe shi".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2811]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi albishir da cewa wanda ƙura ta samu diga-digansa alhali shi yana yaƙi a tafarkin Allah cewa wuta ba zata shafe shi ba.