عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا قَالَ:
أُنْزِلَ عَلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ ابْنُ أَرْبَعِينَ، فَمَكَثَ بِمَكَّةَ ثَلَاثَ عَشْرَةَ سَنَةً، ثُمَّ أُمِرَ بِالْهِجْرَةِ، فَهَاجَرَ إِلَى الْمَدِينَةِ، فَمَكَثَ بِهَا عَشْرَ سِنِينَ، ثُمَّ تُوُفِّيَ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3851]
المزيــد ...
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
An saukarwa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali shi yana da shekara arba'in, ya zauna a Makka shekara goma sha uku, sannan aka umarce shi da yin hijira, sai ya yi hijira zuwa Madina, ya zauna a cikinta shekara goma, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya rasu.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3851]
Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa: An saukar da wahayi ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma an aiko shi alhali shekarunsa arba'in, sai ya zauna a Makka shekara goma sha uku bayan wahayi, sannan aka umarce shi da hijira zuwa Madina, ya zauna a cikinta shekara goma, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya rasu shekarunsa sittin da uku.