+ -

عَنْ النَّوَّاسِ بْنِ سَمْعَانَ الْأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«ضَرَبَ اللهُ مَثَلًا صِرَاطًا مُسْتَقِيمًا، وَعَلَى جَنْبَتَيْ الصِّرَاطِ سُورَانِ، فِيهِمَا أَبْوَابٌ مُفَتَّحَةٌ، وَعَلَى الْأَبْوَابِ سُتُورٌ مُرْخَاةٌ، وَعَلَى بَابِ الصِّرَاطِ دَاعٍ يَقُولُ: أَيُّهَا النَّاسُ، ادْخُلُوا الصِّرَاطَ جَمِيعًا، وَلَا تَتَعَرَّجُوا، وَدَاعٍ يَدْعُو مِنْ فَوْقِ الصِّرَاطِ، فَإِذَا أَرَادَ يَفْتَحُ شَيْئًا مِنْ تِلْكَ الْأَبْوَابِ، قَالَ: وَيْحَكَ لَا تَفْتَحْهُ، فَإِنَّكَ إِنْ تَفْتَحْهُ تَلِجْهُ، وَالصِّرَاطُ الْإِسْلَامُ، وَالسُّورَانِ: حُدُودُ اللهِ، وَالْأَبْوَابُ الْمُفَتَّحَةُ: مَحَارِمُ اللهِ، وَذَلِكَ الدَّاعِي عَلَى رَأْسِ الصِّرَاطِ: كِتَابُ اللهِ، وَالدَّاعِي مِنِ فَوْقَ الصِّرَاطِ: وَاعِظُ اللهِ فِي قَلْبِ كُلِّ مُسْلِمٍ».

[صحيح] - [رواه الترمذي وأحمد] - [مسند أحمد: 17634]
المزيــد ...

Daga Nawwas Dan Sam'an Al’Ansary - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Allah Ya buga wani misali hanya ce madaidaiciya, a gefunan hanyar biyu akwai ganuwowi biyu, a cikinsu akwai budaddun kofofi, akan kofofin akwai sakakkun labulaye, a kofar hanyar akwai wani mai kira yana cewa; Yaku mutane, ku shigo hanyar gaba daya, kada ku karkace, da wani mai kiran kuma yana kira a birbishin hanyar, idan ya yi nufin ya bude wani abu daga wadancan kofofin, zai ce: Kaicanka kada ka bude shi , domin cewa kai idan ka bude shi zaka shige shi. Tafarkin shi ne Musulunci, ganuwowin biyu kuma: Su ne iyakokin Allah, budaddun kofofin kuma: Su ne abubuwan da Allah Ya haramta, wannan mai kiran kuma akan tafarkin: Shi ne littafin Allah, mai kiran kuma a birbishin tafarkin: Mai wa'azin Allah ne (Ajiyoyin Allah) a cikin zuciyar kowane musulmi".

[Ingantacce ne] - - [مسند أحمد - 17634]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa; Allah Ya buga wani misali ga Musulunci da hanya madaidaiciya mikakkiya babu karkata a cikinta, agefan wannan hanyar akwai ganuwowi biyu, to bangwaye da suke kewaye da ita ta fuskarsa su ne iyakokin Allah, wasu budaddun kofofi suna shiga wadannan ganuwowi biyun su ne Abubuwan da Allah Ya haramta, akan wadannan kofofin akwai labulayen da basa bayyanar da wanda yake cikinsu ga mai wucewa akan hanyar, afarkon hanyar akwai wani mai kira yake fuskantar da mutane kuma yake shiryar da su yana ce musu: Ku tafi akansa ba tare da kun karkace zuwa wani bangaren ba, wannan mai kiran duk lokacin da mai tafiya akan tafarkin ya yi niyyar ya bude wani gwargwado mai sauki daga labulayen kofofin sai ya tsawatar masa ya ce da shi: Kaicanka kada ka bude shi! domin cewa kai idan ka bude shi zaka shigeshi kuma ba zaka sami damar kare kanka ba daga shiga, wannan mai kiran shi ne mai wa'azin Allah a cikin zuciyar kowane Musulmi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch اليونانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Musulunci shi ne addinin gaskiya, kuma shi ne tafarki madaidaici wanda zai sadar da mu zuwa Aljanna.
  2. Wajabcin lazimtar iyakokin Allah da abinda Ya halatta da abinda Ya haramta, kuma cewa sakaci a cikinsu yana gadar da halaka.
  3. Falalar Alkur’ani mai girma da kwadaitarwa akan aiki da shi, a cikinsa akwai shiriya da haske da tsira.
  4. Rahamar Allah ga bayinSa da abinda Ya ajiye shi a cikin zukatan muminai na a binda zai hanasu ya kuma wa'azantar da su daga fadawa a cikin halaka.
  5. Allah da rahamarSa Ya sanya shamakin da zai hana bayinSa afkawa cikin sabo.
  6. Daga cikin hanyoyin koyarwa akwai buga misali dan kusantowa da bayyanawa.