Karkasawa:
+ -

عَنِ النَّوَّاسِ بْنِ سِمْعَانَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«البِرُّ: حُسْنُ الخُلُقِ، وَالإِثْمُ مَا حَاكَ فِي صَدْرِكَ، وَكَرِهْتَ أَنْ يَطَّلِعَ عَلَيْهِ النَّاسُ». وَعَنْ وَابِصَةَ بْنِ مَعْبَدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: أَتَيْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: «جِئْتَ تَسْأَلُ عَنِ البِرِّ وَالإِثْمِ»، قُلْتُ: نَعَمْ، قَالَ: «اسْتَفْتِ قَلْبَكَ، البِرُّ: مَا اطْمَأَنَّتْ إلَيْهِ النَّفْسُ، وَاطْمَأَنَّ إلَيْهِ القَلْبُ، وَالإِثْمُ: مَا حَاكَ فِي نَفْسِكَ وَتَرَدَّدَ فِي الصَّدْرِ، وَإِنْ أَفْتَاكَ النَّاسُ وَأَفْتَوْكَ».

[صحيح] - [الحديث الأول: رواه مسلم، والحديث الثاني: رواه أحمد والدارمي.] - [الأربعون النووية: 27]
المزيــد ...

Daga Nawwas Ibnu Sam'an al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«al-Birr shi ne: Kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abin da ya sosu a cikin zuciya, kuma ka ƙi mutane su tsinkaya a kansa».

[Ingantacce ne] - [الحديث الأول: رواه مسلم، والحديث الثاني: رواه أحمد والدارمي] - [الأربعون النووية - 27]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da al-birr da kuma zunubi, sai ya ce: Lallai mafi girman ɗabi'un al-birr su ne kyawawan ɗabi'u tare da Allah ta hanyar jin tsoron Allah, haka tare da halitta ta hanyar jure cuta, da ƙarancin fushi, da shimfiɗar fuska, daddaɗan zance, da sadar da zumunci, da biyayya da tausasawa da kuɓutarwa, da kyakkyawar mu'amala da abokantaka, kuma cewa al-birr shi ne abin da zuciya da rai suka nutsu gare shi. Amma zunubi to abin da ya kaikawo a cikin zuciya na abubuwa masu rikitarwa kuma ya kaikawo ba tare da ƙirji ya samu natsuwa daga gareshi ba, kuma kokwanto ya faru daga gare shi a cikin zuciya, da jin tsoron kasancewarsa zunubi ne, kuma baka son ka bayyanar da shi dan kasancewarsa mummuna a idanuwa da mutanen kirki da cikakkun mutane, hakan domin rai a ɗabi'arsa yana son ganin mutane akan alherinsa, idan rai ya ƙi tsinkaya akan wasu daga cikin ayyukansa to shi zunubi ne babu alheri a cikinsa; ko da mutane sun baka fatawa to kada ka ɗauki fatawarsu muddin dai alamar shubha tana kaikawo a cikin ranka, domin fatawa bata kawar da shubha muddin dai shubhar ingantacciya ce, kuma mai bada fatawa yana bada fatawa ba tare da ilimi ba; amma idan fatawar gini ce akan wani dalili na shari'a to wajibi akan mai neman fatawa shi ne ya koma zuwa gare ta, ko da ƙirjinsa bai budeba gareta ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan kyawawan ɗabi'u; domin kyawawan ɗabi'u suna daga mafi girman ɗabi'un aikin alheri.
  2. Gaskiya da ƙarya al'amarinsu ba ya rikitarwa ga mumini, kai yana sanin gaskiya da hasken da ke cikin zuciyarsa, kuma yana gujewa ƙarya sai ya yi musunta.
  3. Daga alamomin zunubi kaikawon zuciya, da ƙin tsinkayar mutane a kansa.
  4. Sindi ya ce: Wannan a abubuwa masu rikitarwa ne waɗanda mutane ba sa sanin hakikanin ɗayan ɓangarori biyun daga cikinsu; inba haka ba abin umarni da shi acikin shari'a ba tare da bayyanar dalili a cikinsa ba akan saɓanin hakan daga aikin alheri, abin hanawa daga gare shi kamar hakan, babu buƙatuwa a cikinsu zuwa neman bada fatawar zuciya da kuma nutsuwarta.
  5. Wandanda akewa magana a cikin hadisin (su ne) ma'abota nagartacciyar ɗabi'a, ba ma'abota karkatattun zukata ba waɗanda ba sa sanin aikin alheri kuma ba sa ƙin abin ƙi sai dai abinda aka cakuɗa daga son ransu kawai.
  6. Ɗibi ya ce: An ce an fassara al-Birr a cikin hadisin da ma'anoni da yawa, ya fassara shi a wani wuri da abinda ransa ya nutsu kuma zuciyarsa ta nutsu da shi, kuma ya fassara shi a wani wurin daban da imani, a wani wurin kuma da abinda zai kusantoka zuwa ga Allah, a nan da kyakkyawar ɗabi'a, an fassara kyakkyawar ɗabi'a: Da jurewa cuta da ƙarancin fushi da shinfiɗar fuska da daddaɗan zance, dukkansu masu kusantar junane a ma'ana.
Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci الأمهرية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الليتوانية الدرية الصربية الطاجيكية Kinyarwanda المجرية التشيكية الموري Kanadische Übersetzung الولوف Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية الجورجية المقدونية الخميرية
Manufofin Fassarorin
kashe kashe
Kari