kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

Ban bar wata fitina a baya na ba mafi cutar da Maza kamar mata ba.
عربي Turanci urdu
An rubutawa Xan Adam rabonsa a Zina kuma dole sai ya same shi babu Makawa: Idanu suna Zina zianarsu Kallo, Kunnuwa suna Zina Zinar su Sauraro, Harshe yana Zina Zinarsa Magana, Hannu Zinarsa Tavawa, Qafa kuma Zinarta tafiya, Zuciya Kuma tana so da Buri, kuma Farji yana gasgata hakan ko ya qaryata shi
عربي Turanci urdu
"Kada ku nemi ilimi dan ku yi wa malamai alfahari da shi, ko ku yi musu da wawaye da shi*, kuma kada ku nufi bijiro da shi a zababbun majalisai, wanda ya aikata haka to wuta wuta".
عربي Turanci urdu
"Allah Ya buga wani misali hanya ce madaidaiciya*, a gefunan hanyar biyu akwai ganuwowi biyu, a cikinsu akwai budaddun kofofi, akan kofofin akwai sakakkun labulaye, a kofar hanyar akwai wani mai kira yana cewa; Yaku mutane, ku shigo hanyar gaba daya, kada ku karkace, da wani mai kiran kuma yana kira a birbishin hanyar, idan ya yi nufin ya bude wani abu daga wadancan kofofin, zai ce: Kaicanka kada ka bude shi , domin cewa kai idan ka bude shi zaka shige shi. Tafarkin shi ne Musulunci, ganuwowin biyu kuma: Su ne iyakokin Allah, budaddun kofofin kuma: Su ne abubuwan da Allah Ya haramta, wannan mai kiran kuma akan tafarkin: Shi ne littafin Allah, mai kiran kuma a birbishin tafarkin: Mai wa'azin Allah ne (Ajiyoyin Allah) a cikin zuciyar kowane musulmi".
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta wannan ayar: {Shi ne wanda ya saukar maka da littafi daga gareshi akwai ayoyi bayyanannu su ne mafi yawan littafi da wasu masu kama da juna, amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata sai suke bin abinda yake kama da juna daga gareshi dan neman fitina da neman tawilinsa, kuma babu wanda yasan tawilinsa sai Allah, matabbata a cikin ilimi suna cewa mun yi imani da shi dukkansa daga gurin Ubangijinmu ne, Ba mai tinani sai ma'abota hankula} [Aal Imran: 7]. Ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "@Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gareshi to wadannan su ne Allah Ya ambata, to ku gujesu*".
عربي Turanci urdu
"Za'a bijiro da fitintinu akan zukata kamar tabarma kara-kara*, duk zuciyar da aka cakuɗata da su sai ta yi masa baƙin ɗigo, duk zuciyar data musantasu kuwa za’a yi mata farin ɗigo, har su zama akan zukata biyu (nau'i biyu), akan farar zuciya kwatankwacin fal dutse, to wannan fitinar ba zata cutar da ita ba muddin sammai da ƙasa suna nan, ɗayar kuma baƙace ƙirin kamar kifaffiyar ƙwarya, ba ta san wani aikin alheri, kuma bata inkarin wani abin ƙi, sai abinda aka cakuɗa mata na son ranta". Huzaifa ya ce: Kuma na zantar da shi, cewa lallai tsakaninka da su akwai wata kullalliyar ƙofa ta kusa a karya ta, Umar ya ce: Shin karyawa za'a yi kaicanka? Inama dai bude ta za'a yi watakila a dawo da ita, na ce: Kuma na zantar da shi wani labarin da bana galadi ba cewa wannan kofar wani mutum ne da za'a kashe ko ya mutu. Abu Khalida ya ce: Sai na ce wa Sa'ad: Ya Abu Malik, me ake nufi da Aswad Murbadun? Ya ce: Tsananin fari a cikin baki. Ya ce: Sai na ce: To me ake nufi da al-Kuzul mujakkhiya? ya ce: Wacce aka kife.
عربي Turanci Indonisiyanci
Babu wani abu mafi sharri da Mutum yake cikawa, ya ishi Dan Adam ya dan ci wani abu da zai to she hanjinsa, to idan Mutum ba zai iya jurewa ba, to ya kasa cikinsa uku daya don abinci daya don abun sha daya donnumfashinsa.
عربي Turanci urdu
Abubuwa biyu nafi tsoro ga Al-umma ta Al-qur'ani da kuma Nono, Amma tsorona da nono saboda zasu riqa bin kauyuka kuma suna bin son ransu kuma suna barin Sallah, kuma Al-Qur'ani shi ne Munafukai su koyeshi sai su riqa jayayya da muminai da shi
عربي Turanci urdu