عن أسامة بن زيد رضي الله عنهما مرفوعاً: «ما تركت بعدي فتنة هي أضر على الرجال من النساء».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
An rawaito daga Usamat Bn Zaid -Allah ya yarda da su- daga Annabi: "Banbar wata Fitina a bayana ba wacce tafi cutar da Maza kamar Mata"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Annabi -Amincin Allah a gare shi- ya bada labari cewa Mata sune babban sanadin fitinar Maza, wannan ta hanayar rudarsu da jawo su ga barin gaskiya idan suka futo suka cudanya da Maza, kuma idan kadaicewa ta faru da su, Cutar a nan tana Kasancewa ne a lahira da kuma Duniya