عَنْ ابْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهُما أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَا حَقُّ امْرِئٍ مُسْلِمٍ لَهُ شَيْءٌ يُوصِي فِيهِ، يَبِيتُ ثَلَاثَ لَيَالٍ، إِلَّا وَوَصِيَّتُهُ عِنْدَهُ مَكْتُوبَةٌ»، قَالَ عَبْدُ اللهِ بْنُ عُمَرَ رضي الله عنهما: «مَا مَرَّتْ عَلَيَّ لَيْلَةٌ مُنْذُ سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ ذَلِكَ إِلَّا وَعِنْدِي وَصِيَّتِي».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1627]
المزيــد ...
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ba ya kamata ga wani mutum musulmi da yake da wani abinda zai yi wasiyya da shi, ya kwana darare uku sai wasiyyarsa tana rubuce a wurinsa", Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: "Wani dare bai taɓa wucewa gareni ba tunda na ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya faɗi haka ba sai wasiyyata tana tare da ni".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1627]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ba ya kamata ga wani musulmi da yake da wani abinda zai yi wasicci da shi na haƙƙoƙi ko dukiyoyi koda kaɗan ne, ya kwana darere uku, sai wasiyyarsa tana rubuce a wurinsa. Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - Ya ce: Ban taɓa kwana a wani dare ba tunda na ji shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi haka sai wasiyyata tana tare da ni.