+ -

عن سعد بن أبي وقاص رضي الله عنه قال: جاءني رسول الله صلى الله عليه وسلم يَعُودُنِي عام حَجَّةِ الوداع من وَجَعٍ اشْتَدَّ بي، فقلت: يا رسول الله، قد بلغ بي من الوَجَعِ ما ترى، وأنا ذو مال، ولا يَرِثُنِي إلا ابنةٌ أَفَأَتَصَدَّقُ بثلثي مالي؟ قال: لا، قلت: فالشَّطْرُ يا رسول الله؟ قال: لا، قلت: فالثلث؟ قال: الثلث، والثلث كثير، إنك إن تَذَرَ وَرَثَتَكَ أغنياء خيرٌ من أن تَذَرَهُم عالَةً يَتَكَفَّفُونَ الناس، وإنك لن تنفق نفقة تبتغي بها وجه الله إلا أُجِرْتَ بها، حتى ما تجعل في فِيْ امرأتك. قال: قلت: يا رسول الله أُخَلَّفُ بعد أصحابي؟ قال: إنك لن تُخَلَّفُ فتعمل عملا تبتغي به وجه الله إلا ازْدَدْتَ به درجة ورِفْعَةً، ولعلك أن تُخَلَّفَ حتى ينتفع بك أقوام، ويُضَرُّ بك آخرون. اللهم أَمْضِ لأصحابي هجرتهم، ولا تَرُدَّهُم على أَعْقَابِهِم، لكنِ البَائِسُ سعد بن خَوْلَةَ (يَرْثِي له رسول الله صلى الله عليه وسلم أن مات بمكة).
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

An karbo daga Sa'ad Dan Abi Wakkas-Allah ya yarda da shi-yace:Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yazo min don ya dubani shekarar Hajjin ban-kwana daga wani ciwo da yayi tsanani agareni,sai nace:Ya Ma'aikin Allah,hakika ciwo yakai inda yakai agareni kamar yadda kake gani,kuma ni Ma'abocin Dukiya ne,bamai gadona sai 'ya mace bana yi Sadaka da Biyu bisa Ukun Dukiyata ba?yace:a'a,nace:Rabi fa ya Ma'aikin Allah?yace:a'a,nace:Daya bisa Ukufa?yace:Daya bisa Uku,kuma Daya bisa Uku da yawa,hakika cewa kai kabar Magadanka Mawadata shi yafi akan kabarsu Talakawa suna rokon Mutane,kuma cewa kai ba zaka ciyar da wata ciyarwa ba kana mai neman Fuskar Allah face Allah ya baka lada da ita,hatta abinda zaka saka a Bakin Matarka.Yace:Nace ya Ma'aikin Allah zan barwa abokanaina a bayana?yace:Hakika cewa kai ba za'a barka ba ka aikata wani aiki da kake neman Fuskar Allah sai ka kara Daraja dashi da Daukaka,kuma watakila kuma idan aka barka har wasu su amfana da kai wasu kuma su cutu da kai,ya Allah ka cikawa Abokanaina Hijirarsu,kada ka juyar dasu a bayansu,sai dai sadauki shine Sa'ad Dan Khaula(Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana yi masa Rasa'i don ya Rasu a Makka)
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Sa'ad Dan Abi Wakkas Allah ya yarda dashi yayi rashin lafiya lokacin Hajjin ban kwana rashin lafiya maitsanani wacce saboda tsananinta yaji tsoran Mutuwa Sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya duba shi kamar yadda al'adarsa take cikin bibiyar Sahabansa da jajantawa a garesu Sai Sa'ad ya ambatawa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi damuwoyinsa, abinda ya kudira na cewa zai Sadaka da dukan Dukiyarsa, sai yace: Ya Ma'aikin Allah, hakika ciwo mai tsanani yayi tsanani agareni wanda nake jin tsoran Mutuwa daga gareshi, kuma ni ma'abocin Dukiya mai yawa ne, kuma cewa shi babu daga Magada Raunana wadanda nake tsoran talauci da tozarta a kansu face 'yata Guda daya, to bayan wannan shin na iya Sadaka da Biyu bisa Uku na Dukiyata, don na gabatar dashi ga managarcin aikina? sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace: a'a Yace: Rabi fa ya Ma'aikin Allah? yace: a'a yace: Daya bisa uku fa? sai yace: ba abinda zai hanaka Sadaka da Daya bisa uku duk da cewa mai yawa ne Domin cewa saukowa izuwa abinda yake koma bayansa na daga Daya bisa Hudu ko Daya bisa biyar shi yafi Sannan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya bayyana masa Hikima cikin saukowa cikin Sadaka da mafi yawan Dukiya izuwa mafi karancinta da lamari Biyu: 1. shine cewa shi in ya mutu alhali ya bar Magadansa Mawadata masu amfani da Nagartarsa da Dukiyarsa to hakan shi yafi akan ya fitar dashi daga garesu izuwa waninsu, ya barsu suna rayuwa abisa kyautayin Mutane. 2. ko kuma a wanzar dashi ya sami Dukiyarsa, sai ya ciyar da ita ta hanyoyin da Shari'a ta shara'anta, kuma ya nemi lada awajan Allah sai a saka masa abisa hakan, har acikin abinda yake mafi wajabcin ciyarwa akansa shine abinda zai ciyar da Matarsa Sannan Sa'ad Dan Abi Wakkas yaji tsoran ya mutu a Maka wacce yayi Hijira daga gareta ya kuma barta saboda Allah Madaukaki, sai yin hakan ya tauye masa wani abu daga sakamakon Hijirarsa, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya bashi Labari cewa ba za'a barshi bisa dole a cikin Garin da yayi Hijira daga gareshi ba, sannan yayi wani aiki acikinsa don neman ladan Allah face ya kara Daraja da shi, sannan Annabi tsira da abincin Allah su tabbata agareshi yayi masa Bushara da abinda yake nuni da cewa zai warke daga ciwonsa, Allah ya amfani Muminai dashi, ya kuma cutar da Kafirai dashi,sai hakan ta kasance kamar yadda Mai Gaskiya abin Gasgatawa ya bada labari, sai ya warke daga rashinlafiyarsa, kuma ya zama Jagora mafi Girma acikin yakin Farisawa, kuma Allah ya amfani Musulunci da Musulmai dashi, yayi Bude Bude kuma Allah ya cutar da Shirka da Mushirikai dashi, sannan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya yiwa Sahabbansa Addu'a cewa ya tabbatar musu da Darajarsu, ya kuma karbeta daga garesu, kuma kada suyi Ridda a cikin Addininsu ko kuma kar ya mayar dasu Garin da suka yi Hijira daga gareshi, sai Allah ya karbi hakan daga gareshi, Godiya da Baiwa tasa ce, kuma dukkan Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya Daukaka Musulunci dasu Sannan ya ambaci Sa'ad Dan khaula,shi yana cikin masu kaura wadanda sukayi kaura daga Maka sai dai Allah ya kaddara cewa zai mutu acikinta, sai ya mutu kuwa acikin nata, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi masa Rasa'i: ana nufin: bai ji masa dadi ba saboda ya mutu a Maka; hakika sun kasance suna ki ga wanda yayi Hijira ya mutu a Kasar da yayi Hijira daga gareta.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Portuguese
Manufofin Fassarorin