عَنْ عَلِيٍّ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ مُكَاتَبًا جَاءَهُ، فَقَالَ: إِنِّي قَدْ عَجَزْتُ عَنْ مُكَاتَبَتِي فَأَعِنِّي، قَالَ: أَلاَ أُعَلِّمُكَ كَلِمَاتٍ عَلَّمَنِيهِنَّ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، لَوْ كَانَ عَلَيْكَ مِثْلُ جَبَلِ صِيرٍ دَيْنًا أَدَّاهُ اللَّهُ عَنْكَ، قَالَ:
«قُلْ: اللَّهُمَّ اكْفِنِي بِحَلاَلِكَ عَنْ حَرَامِكَ، وَأَغْنِنِي بِفَضْلِكَ عَمَّنْ سِوَاكَ».
[حسن] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 3563]
المزيــد ...
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - cewa wani wanda aka ɗorawa fansa ya zo masa, sai ya ce: Haƙiƙa ni na kasa biyan fansa ta to ka taimakeni, ya ce: Shin bana sanar da kai wasu kalmomi ba waɗanda mazon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da ni su, da a ce kana da bashi a kanka kwatankwacin dutsen Seer Allah Zai biya maka, ya ce:
"Ka ce : Ya Allah Ka wadatar da ni da halalinKa daga barin haram ɗinKa, kuma Ka wadatani da falalarKa daga wanda ba Kai ba".
[Hasan ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi] - [سنن الترمذي - 3563]
Wani bawa wanda mai shi ya ɗorawa fansa kuma ya yi ittifaƙi tare da shi akan ya sayi kansa ya 'yantata dan ya zama ɗa, kuma ba shi da dukiya, ya zo wurin sarkin muminai Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: Haƙiƙa ni na gajiya (na kasa) daga biyan abinda ke kaina to ka taimakeni akan biyansa da dukiya, ko da koyarwa da shiryarwa, sai sarkin muminai ya ce masa; Shin bana sanar da kai wasu kalmomi ba waɗanda manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani su, da a ce a kanka akwai bashi kwatankwacin wani dutse mai suna Seer na ƙabilar Ɗayyu ne da Allah Ya biya maka shi zuwa ga mai shi, kuma Ya tsamoka daga ƙasƙancinsa, Ya ce: Ka ce: (Ya Allah Ka isar mini) Ka juyar mini Ka nisantar da ni (da halal ɗinKa) ina mai wadatuwa da ita, (daga) faɗawa a (haram ɗinKa), (Kuma Ka wadatar da ni) Ka isar mini (da falalarKa) samuwarKa (daga wanda ba Kai ba) cikin halitta.