+ -

عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ:
كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَسْتَحِبُّ الْجَوَامِعَ مِنَ الدُّعَاءِ، وَيَدَعُ مَا سِوَى ذَلِكَ.

[صحيح] - [رواه أبو داود وأحمد] - [سنن أبي داود: 1482]
المزيــد ...

Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son Addu'ar da ta tattaro komai, kuma yana ƙyale wacce ba ita ba.

[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 1482]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son addu'o'i masu tattaro alherin duniya da lahira wacce lafazinta kaɗan ne kuma ma'anarta yana da yawa, kuma a cikinta akwai yabo ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da manufofi na gari, kuma yana barin koma bayan haka.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so addu'a da lafuza sassauƙa masu tattaro ma'anonin alheri, da kuma ƙin ɗorawa kai wahala da tsananatawa a cikin mas'ala, hakan saɓanin karantarwar Annabi ce - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  2. An keɓanci Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kalmomi masu tattaro (ma'anoni).
  3. Kwaɗayi akan abinda ya tabbata cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da shi; koda ya kasance mai tsawo ne, kuma kalmominsa sun yi yawa, dukkansa daga addu'o'i ne masu tattarowa.