عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«أَلْحِقُوا الفَرَائِضَ بِأَهْلِهَا، فَمَا بَقِيَ فَلِأَوْلَى رَجُلٍ ذَكَرٍ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6737]
المزيــد ...
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Ku riskar da (kason gado) ta hanyar farillai ga ma'abotansu, abin da ya rage to namiji makusanci shi ne ya fi cancantarsa ».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6737]
Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- ya umarci masu raba gado da su raba wa waɗanda suka cancanci rabon bisa adalci kamar yadda sharia ta yi bayani, kamar yadda Allah Yake nufi, sai a baiwa magada abin da Allah ya kaddarawa kowa a cikin Littafinsa, shi ne biyu cikin uku, da ɗaya cikin uku, da ɗaya cikin shida, da Rabi, da ɗaya cikin huɗu, da ɗaya cikin takwas. Abin da ya yi saura bayan wannan, to sai a baiwa mafi kusanci ga mamacin daga cikin maza; su ake kira Asubai.