+ -

عن عقبة بن عامر رضي الله عنه مرفوعاً: «إياكم والدخولَ على النساء، فقال رجل من الأنصار: يا رسول الله، أرأيتَ الحَمُو؟ قال: الحَمُو الموتُ». ولمسلم: عن أبي الطاهر عن ابن وهب قال: سمعت الليث يقول: الحمو: أخو الزوج وما أشبهه من أقارب الزوج، ابن عم ونحوه.
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Ukuba Dan Amir -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Na haneku ga barin shi da kadaita da Mata, sai wani Mutumin Madina ya ce: Ya Manzon Allah, Baka ganin Miji? ai ya ce: Kanin Miji ai Mutuwa ke nan" kuma a wata riwayar ta Muslim: daga Abu Dahir daga Abuwahb ya ce: naji Allaith yana cewa: Kanin Miji: yana nufin Dan uwan Miji da kuma duk wanda yake matsayinsa na Yan uwan Miji, Kamar Dan Baffansa da Mai kama da shi.
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi ya tsawatar da mu ga barin shiga wurin mata wadanda basu halatta a gare mu ba, da kuma kadaita da su domin cewa Namiji bai kadaita da Mace ba face Shaidan ya zama na ukunsukuma cewa zukata raunana ne, kuma dalilan da suke jan mutum ya fada Sabo suna da karfi, sai Sabo ya wakana don haka ya hana kadaita din da su daga barin sharri da kuma Abubuwan da suke jawo shi. sai wani Mutum ya ce: to ya Manzon Allah ka bamu labarin kanin Miji mana wanda shi makusancin Miji, don watakila wani lokaci in bukace shi don ya shiga gidan Dan uwansa kuma a halin Matarsa tana ciki, ko akawai rangwame akansa? Sai Annabi ya ce: Kanin Miji ai Mutuwa ke nan domin Mutane sakacin shigarsa kuma basa hana shi, sai ya kadaita da matar da bata halatta a gareshi ba, kuma sau da yawa Alfasha tana faruwa a hakan kuma hakan yayi ta faruwa ba tare da ansani ko anyi zargin hakan, sai ya kasance Addini ya rushe, kuma rushewa na dindindin, kuma bashi da wani sauki, kawai dai ku kiyayi hakan daga barin kadaitar Matanku da shi, indai ku masu kishi ne.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin