عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي لله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا يَفْرَكْ مُؤْمِنٌ مُؤْمِنَةً، إِنْ كَرِهَ مِنْهَا خُلُقًا رَضِيَ مِنْهَا آخَرَ» أَوْ قَالَ: «غَيْرَهُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1469]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kada wani mumini ya ki wata mumina, in ya ki wata ɗabi’ar daga gareta to zai so wata ɗabi’ar daga gareta Ko ya ce: "Waninsa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1469]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana miji ya ki matarsa ƙin da zai kai zuwa ga zalinci da barinta da bijire mata; Domin mutum an halicce shi ne akan tawaya, idan ya ki wata mummunar ɗabi'a daga gareta, to zai samu wata kyakkyawar ɗabi'ar a tare da ita; sai ya yarda da mai kyan da ta dace da shi, kuma ya yi haƙuri akan wadda bai yarda ba ta munanar, abinda zai sa shi ya yi haƙuri kada ya ki ta ƙiyayyar da zata ɗauke shi akan rabuwa da ita.