lis din Hadisai

Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa.
عربي Turanci urdu
Mafi cancantar sharuɗɗa da za ku cika; su ne wadanda aka halatta muku mata da su.
عربي Turanci urdu
Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya mana jawabin fara magana*: Lalle godiya ta tabbata ga Allah, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna neman tsari daga sharrin kawunammu, wanda Allah Ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda ya ɓatar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, ina kuma shaidawa [Annabi] Muhammad bawanSa ne, kuma ManzonSa ne. {Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku, Wanda Ya halicceku daga rai guda ɗaya, Ya halitta masa matarsa daga shi, daga su ya yaɗa maza da yawa da mata, Ku ji tsoron Allah Wanda ku ke magiya da Shi, (ku kiyaye) da zumunta, lalle Allah Ya kasance Mai kula da ku ne}. {Ya ku waɗanda ku ka yi imani ku ji tsoron Allah haƙiƙanin jin tsoronSa, kada ku mutu face kuna Musulmai}. {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, ku faɗi magana ta daidai, zai gyara muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubanku, duk wanda Ya yi wa Allah da ManzonSa biyayya, to, haƙiƙa ya rabauta, rabauta mai girman gaske.
عربي Turanci urdu
"Babu aure sai da waliyyi".
عربي Turanci urdu
"Kada wani mumini ya ki wata mumina, in ya ki wata ɗabi’ar daga gareta to zai so wata ɗabi’ar daga gareta* Ko ya ce: "Waninsa".
عربي Turanci urdu
"Idan Mutum ya kirawo Matarsa saboda bukatarsa to taje masa kuma ko da ta kasance takan Tanderu ne"
عربي Turanci urdu
"Dukkaninku masu kiwone to abin tambayane daga abinda yake kiwonta,* shugaban mutane mai kiwo ne shi abin tambayane game da su, mutum mai kiwone ga iyalan gidansa kuma shi abin tambaya ne game da su, mace mai kiwo ce a dakin mijinta da ’yayansa kuma ita abar tambaya ce game da su,, bawa mai kiwo ne akan dukiyar shugabansa shi abin tambaya ne game da ita, ku saurara dukkaninku abin tambaya ne game da abin da aka ba shi kiwonsa".
عربي Turanci urdu
"Duk wanda yake da iko a cikinku to ya yi aure, domin cewa shi ne yafi rintse ido, kuma ya fi katange farji, wanda ba zai iya ba to na umarce shi da azimi, domin shi kariyane gare shi".
عربي Turanci urdu
Ba'a Aurar da Bazawara har sai an nemi Izininta, kuma ba'a Aurar da Budurwa har sai an sai ta yarda, sai suka ce Ya Manzon Allah to ta yaya za'a gane yardar ta sai ya ce: Shi ne tayi shiru.
عربي Turanci urdu
“Duk macen da ta yi aure ba tare da izinin waliyinta ba, to aurenta ɓatacce ne - sau uku - idan ya tare da ita, to sadakin ya kasance nata ne saboda abinda ya samu na (jima'i) daga gareta, idan suka yi jayayya to sarki (shi ne) waliyyin wanda ba shi da waliyyi".
عربي Turanci urdu
"Wanda ya zo wa matarsa ta duburarta tsinanne ne".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace".
عربي Turanci urdu
Ku kula da mata da kyau; Don mace an halicce ta ne daga haƙarƙari, kuma idan haƙarƙarin ya karkace sama da ita, idan ka je, zai saita ta, kuma idan ka bar ta, har yanzu ta karkace, don haka nemi shawara daga mata. Kuma a cikin wata ruwaya: "Mace kamar haƙarƙari take, idan ta daga shi, sai ta karye, idan kuma ta ji daɗin ta, sai ta ji daɗin kuma akwai wani gaɓa.
عربي Turanci urdu
Dayanku yana yin baftisma kuma ya yi wa matarsa d thekan d ofkan wani bawa, don haka watakila zai kwana da ita daga ƙarshen ranar
عربي Turanci urdu
Daga cikin mafiya sharrin mutane akwai matsayi a wurin Allah ranar tashin kiyama. Namiji ne ya kai wa ga matar ya sadar da shi gare shi, sannan ya buga shi
عربي Turanci urdu
«‌Kada ku daki bayin Allah mata» sai Umar ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Mata sun yi wa mazajensu tawaye, sai ya yi rangwami a dukansu, sai mata da yawa suka kewaye iyalan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna kawo ƙarar mazajensu, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: @«‌Haƙiƙa mata da yawa sun kewaye iyalan (Annabi) Muhammad suna kawo ƙarar mazajensu to waɗannan ba zaɓaɓɓunku ba ne».
عربي Turanci urdu
"Wata Mace bata taba Cutar Mijinta a Duniya ba sai Matar sa ta Hur Al'aini ta ce kada ki cuce shi Allah ya tsine miki saboda a wajenki bako ne ya kusa da ya rabu dake zuwa gare mu"
عربي Turanci urdu
"Da zan Umarci wani Mutum da yayi sujada ga wani wallahi da na Umarci Mace ta yi Sujada ga Mijinta"
عربي Turanci urdu
Cewa Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su Tabbata a gareshi- ya hana Auren Musanye
عربي Turanci urdu
"Ya Manzon Allah wata Mata tayi Aure, sai ya ce: "Mai ka bata Sadaki? ya ce: Awan Kwallon Dabino na zinare ya ce: "Allah ya yi Maka al-barka", kayi walima koda da Akuya ne"
عربي Turanci urdu
An anbaci Azalu ga Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- sai ya ce: Kuma babu dayanku da ya aikata ta? saboda babu wani rai da Allah ya halitta sai ya halicceta"
عربي Turanci urdu
Annabi-Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- ya hana Usman Dan Mazoun Kyamar Aure don Ibada kawai, da kuma yai masa Izini da Mun kebanta da shi
عربي Turanci urdu
"Mun kasance Munayin Azalu kuma Qurani yana sauka, sufyan: da ace abu ne da aka hana da Qur'ani ya Hanamu"
عربي Turanci urdu
Ba'a hada tsakanin Mace da gwaggwanta ko kuma tsakaninta da Innar ta
عربي Turanci urdu
Yana daga sunna in ya auri budurwa: sai ya yi kwana bakwai a dakinta sannan ya raba kwana, in kuma bazawara ya aura sai yayi kwana uku a wajenta sannan ya raba kwana
عربي Turanci urdu
Daga Abdullahi Dan Abbas-Allah ya yarda da shi- ya ce Manzon Allah-tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce game da 'Diyar Hamza: "Bata halatta a gare ni ba, domin shayarwa ta haramta abin da nasaba take haramtawa, kuma ita Diyar Dan uwana na shayarwa ne
عربي Turanci urdu
"Cewa Annabi ya hana Auren Mutu'a a Ranar yakin Khaibara, da kuma cin Naman Jakin gida"
عربي Turanci urdu
Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi- Ya 'yanta Safiyya, kuma ya sanya Yancinta shi ne Sadakinta"
عربي Turanci urdu