عَنْ مُعَاوِيَةَ الْقُشَيْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ:
قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، مَا حَقُّ زَوْجَةِ أَحَدِنَا عَلَيْهِ؟، قَالَ: «أَنْ تُطْعِمَهَا إِذَا طَعِمْتَ، وَتَكْسُوَهَا إِذَا اكْتَسَيْتَ، أَوِ اكْتَسَبْتَ، وَلَا تَضْرِبِ الْوَجْهَ، وَلَا تُقَبِّحْ، وَلَا تَهْجُرْ إِلَّا فِي الْبَيْتِ»
[حسن] - [رواه أبو داود وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 2142]
المزيــد ...
Daga Mu'awiyya alKushairi - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a kansa?, ya ce;
"Ka ciyar da ita idan kaci, ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), ko ka yi aiki, kada ka daki fuska, kada ka munana, kuma kada ka ƙaurace sai a ɗaki".
[Hasan ne] - - [سنن أبي داود - 2142]
An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - menene haƙƙin mata akan mijinta? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wasu al'amura, daga cikinsu:
Na farko: Kada ka keɓanci kanka da abin ci banda ita; kai ka ciyar da ita a duk lokacin da ka ci abin ci.
Na biyu: Kada ka keɓanci kanka da tufatarwa da tufafi, kai ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), hak idan ka yi aiki kuma ka samu iko.
Na uku: Ba'a dukanta sai da wani sababi da buƙatuwa, idan ya buƙatu zuwa dukanta dan ladabtarwa ko dan barinta wasu farillai to sai ya zama duka ba mai sa rauni ba; kuma ba'a dukan fuska; domin cewa fuska ita ce mafi girman gaɓɓai kuma mafi bayyanarsu kuma ta ƙunshi wasu sasanni manya da gaɓɓai masu laushi.
Na huɗu: Kada ka yi zagi ko ka ce : Allah Ya munana fuskarki; kada ka danganta koda wani abu daga jikinta zuwa munin da shi ne kishiyar kyau; domin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Shi ne wanda Ya suranta fuskar mutum da jikinsa, kuma Ya kyautata halittar kowane abu, zargin halitta yana komawa ne zuwa zargin Mahalicci tsarki ya tabbata ga Allah.
Na biyar: Kada ka ƙaurace sai a wurin kwanciya, kuma kada ka juya mata baya, kada ka juyar da ita zuwa wani gidan daban; wataƙila hakan a cikin abinda afkuwarsa yake sabawa ne daga ƙauracewa tsakanin miji da mata.