عن أبي موسى رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«لا نِكَاحَ إِلّا بِوَليٍّ».

[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد]
المزيــد ...

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Babu aure sai da waliyyi".

Ingantacce ne - Ibnu Majah ne ya Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa mace auranta ba ya inganta sai da waliyyin da zai tsaya a ɗaurin auren.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Waliyyi sharaɗi ne a ingancin aure, idan aure ya faru ba tare da waliyyi ba, ko mace ta aurar da kanta, to, aurenta bai inagnta ba.
  2. Waliyyi shi ne mafi kusancin mazaje ga mace, wani waliyyi na nesa ba zai aurar da ita ba, tare da samuwar waliyyi na kusa.
  3. An sharɗanta (wasu) sharuɗɗa ga waliyyi: Ya zama mukallafi, kuma namiji, da shiriya a sanin maslahohin aure, da haɗuwar Addini tsakanin waliyyi da wanda zai yi wa walicci, duk wanda bai siffantu da waɗannan siffofin ba, to bai cancanci zama waliyyi a ɗaura aure ba.