+ -

عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال:
عَلَّمَنَا رَسُوْلُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خُطْبَةَ الحَاجَةِ: إِنَّ الحَمْدَ للهِ، نَسْتَعِيْنُهُ وَنَسْتَغْفِرُهُ، وَنَعُوْذُ بِهِ مِنْ شُرُوْرِ أَنْفُسِنَا، مَنْ يَهْدِ اللهُ فَلَا مُضِلَّ لَهُ، وَمَنْ يُضْلِلْ فَلَا هَادِيَ لَهُ، وَأَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا الله، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُوْلُهُ، {يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْسٍ وَاحِدَةٍ وَخَلَقَ مِنْهَا زَوْجَهَا وَبَثَّ مِنْهُمَا رِجَالًا كَثِيرًا وَنِسَاءً وَاتَّقُوا اللَّهَ الَّذِي تَسَاءَلُونَ بِهِ والأرحام إن الله كان عليكم رقيبا} [النساء: 1]، {يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ حَقَّ تُقَاتِهِ وَلَا تَمُوتُنَّ إِلَّا وَأَنْتُمْ مُسْلِمُونَ} [آل عمران: 102]، {يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَقُولُوا قَوْلًا سَدِيدًا (70) يُصْلِحْ لَكُمْ أَعْمَالَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَمَنْ يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ فَازَ فَوْزًا عَظِيمًا} [الأحزاب:70 - 71].

[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه والنسائي وأحمد] - [سنن أبي داود: 2118]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi:-
Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya mana jawabin fara magana: Lalle godiya ta tabbata ga Allah, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna neman tsari daga sharrin kawunammu, wanda Allah Ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda ya ɓatar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, ina kuma shaidawa [Annabi] Muhammad bawanSa ne, kuma ManzonSa ne. {Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku, Wanda Ya halicceku daga rai guda ɗaya, Ya halitta masa matarsa daga shi, daga su ya yaɗa maza da yawa da mata, Ku ji tsoron Allah Wanda ku ke magiya da Shi, (ku kiyaye) da zumunta, lalle Allah Ya kasance Mai kula da ku ne}. {Ya ku waɗanda ku ka yi imani ku ji tsoron Allah haƙiƙanin jin tsoronSa, kada ku mutu face kuna Musulmai}. {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, ku faɗi magana ta daidai, zai gyara muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubanku, duk wanda Ya yi wa Allah da ManzonSa biyayya, to, haƙiƙa ya rabauta, rabauta mai girman gaske.

[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 2118]

Bayani

Dan Mas’ud Allah Ya yarda da shi, yana ba da labarin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya musu huɗubar buƙata, wato wadda ake faɗa lokacin buɗe magana a huɗubobi, da kuma kafin faɗin buƙatar mai jawabi, kamar huɗubar aure da huɗubar Juma’a da sauransu. Wannan huɗubar ta ƙunshi ma’anoni masu girman gaske na bayanin cacncantar Allah ga dukkanin nau’o'in yabo, da neman taimakonSa Shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, da neman yafiyar zunubai da kankarewsu , da neman kariyarSa daga dukkan sharri, da sharrin kai da sauransu.
Sannan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ba da bayanin, ita shiriya tana hannun Allah ne, wanda kuma Ya shiryar da shi, to, babu mai ɓatar da shi, wanda kuma ya ɓatar, to, babu mai shiryar da shi.
Sannan ya ambaci shaidawa da Tauhidi, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, da shaidawa da Manzanci da cewa Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) bawanSa ne kuma manzanSa ne.
Sai Kuma ya rufe wannan huɗubar da ayoyi guda uku waɗanda suka ƙunshi umarni da jin tsoron Allah maɗaukaki ta hanyar aikata umarninSa da kuma nisantar abin da Ya hana don neman yardar Allah, kuma sakamakon wanda ya aikata haka kyautatuwan ayyuka da maganganu da kankarewar zunubi da gafarta laifuka, da kuma kyakyawar rayuwa a duniya, da rabauta da aljanna ranar Alƙiyama.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so buɗe huɗubar aure da Juma’a da waninsu da wannan jawabin.
  2. Ya kamata Huɗuba ta ƙunshi yabo ga Allah, da shaidawa biyu, da kuma wasu ayoyi na Alƙur’ani.
  3. Koyarwar da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya yi wa sahabbansa na abin da suke buƙata na lamuran addininsu.