+ -

عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «لا تنُكْحَ ُالأيُّم حتى تُستأمر، ولا تنكح البكر حتى تُستَأذن، قالوا: يا رسول الله، فكيف إذنها قال: أن تسكت».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Annabi: "Ba'a Aurar da Bazawara har sai an nemi Izininta, kuma ba'a Aurar da Budurwa har sai an sai ta yarda, sai suka ce Ya Manzon Allah to ta yaya za'a gane yardar ta sai ya ce: Shi ne tayi shira"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Daurin Aure wani abu ne da yake da matukar hadari, yana halatta mafi tsadar abinda mace take kiyayewa, shi ne farjinta, kuma tana kasancewa sabida wannan Auren baiwa ga Mijinta, don haka sharia ta sanya mata Adalci da kuma jin kai da kuma Hikima kan ta zabi abokin zaman rayuwarta, kuma ta zabe shi da ganinta domin ita take son ta zauna da shi, kuma ita ce mafi sani da abinda tafi karkata da wanda take bukata. don haka Annabi don haka Annabi ya hana a aurar da bazawara har sai anji daga bakinta sannan kuma ta yarda, kamar yadda ya hana a aurara da Budurwa sai ta yadda ita ma kuma ta yi izinin hakan, kuma sabida cewa Budurwa tana da tsananin kunya sharia ta takaita da mafi saukin abu na daga Al'amarinta, kuma shi ne Izini, kamar yadda ta wadata da yin shirun ta kuma ya nuna yardar ta ne.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin