عَنْ أُمِّ عَطِيَّةَ رَضيَ اللهُ عنها أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَا تُحِدُّ امْرَأَةٌ عَلَى مَيِّتٍ فَوْقَ ثَلَاثٍ إِلَّا عَلَى زَوْجٍ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا، وَلَا تَلْبَسُ ثَوْبًا مَصْبُوغًا إِلَّا ثَوْبَ عَصْبٍ، وَلَا تَكْتَحِلُ، وَلَا تَمَسُّ طِيبًا إِلَّا إِذَا طَهُرَتْ نُبْذَةً مِنْ قُسْطٍ أَوْ أَظْفَارٍ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 938]
المزيــد ...
Daga Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Mace ba zata yi idda ga mamaci sama da kwana uku ba, sai ga miji wata huɗu da kwana goma, kuma kada ta sanya tufa rinanniya sai tufa na asb (wasu tufafi ne na Yaman masu fari da baƙi), kuma kada ta sa kwalli, kuma kada ta shafa tirare sai dai idan ta yi tsarki sai ta shafa wani gutsire na tiraren ƙusɗ ko azfar».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 938]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani ga mai idda (takaba) daga barin ado na tirare da kwalli da kayan ado da kyawawan kayan sawa ga mamaci sama da kwana uku, uba ne ko ɗan'uwa ko ɗa ko wasunsu, sai ga miji kawai wata huɗu da kwana goma, kuma alokacin iddarta (takaba) ga miji, kar ta sanya dukkanin rinannun tufafi dan yin ado sai tufafin asb, shi ne tufa na Yaman wanda ake rinawa kafin a saƙa shi, kuma kada ta sa kwalli a ido dan yin ado, kada ta shafa tirare mai ƙanshi da waninsu, sai dai idan ta yi wankan haila, sai ta shafa wani gutsire ƙarami na tiraren ƙusɗ ko azafar, su wasu nau’uka ne sanannu na tiraren wuta, basu zama daga manufar shafa tirare ba, an yi rangwami a cikinsa ga wacce ta yi wankan daukewar al’ada dan kawar da warin da ba'a so, da zata bibiyi gurbin jini da shi a acikin farji ba dan shafa tirare ba.