+ -

عن زينب بنت أبي سلمة قالت: تُوُفِّيَ حَمِيْمٌ لأم حبيبة، فدعت بصُفْرَةٍ، فَمَسحَتْ بذراعيها، فقالت: إنما أصنع هذا؛ لأني سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «لا يحل لامرأة تؤمن بالله واليوم الآخر أن تُحِدَّ على ميت فوق ثلاث، إلا على زوج: أربعة أشهر وعشرًا».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Hamim ya Mutu ya bar Ummu Habiba sai tasa aka kawo mata wani abu mai rawaya, sai ta shafe hannunta, sai tace: cewa nayi wannan ne; domin naji Annabi yana cewa: "Bai halatta ga Mace ba tayi Imani da Allah da kuma ranar lahira tayi Takabar mutuwa sama da da uku, sai dai in akan Miji ne: Wata hudu da kwana goma"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Mahaifin Ummu Habiba ya rasu, kuma ta kasance taji hanin yin takaba sama da Uku sai akan miji, sai ta so tabbatar da aiki da wannan Hadisi, sai ta nemi akawo mata turare wanda yake an cudanya shi da wani abu rawaya, sai ta shafi dantsenta, kuma tayi bayanin abinda ya sanya ta ta saka Turaren kuma shi cewa ita taji Annabi yana cewa: "Bai halatta ga Mace ba tayi Imani da Allah da kuma ranar lahira tayi Takabar mutuwa sama da da uku, sai dai in akan Miji ne: Wata hudu da kwana gom"

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin