+ -

عَنْ أَبَانَ بْنِ عُثْمَانَ قَالَ: سَمِعْتُ عُثْمَانَ ابْنِ عَفَّانَ رضي الله عنه يَقُولُ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«مَنْ قَالَ بِسْمِ اللَّهِ الَّذِي لَا يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ، فِي الْأَرْضِ، وَلَا فِي السَّمَاءِ، وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ، ثَلَاثَ مَرَّاتٍ، لَمْ تُصِبْهُ فَجْأَةُ بَلَاءٍ، حَتَّى يُصْبِحَ، وَمَنْ قَالَهَا حِينَ يُصْبِحُ ثَلَاثُ مَرَّاتٍ، لَمْ تُصِبْهُ فَجْأَةُ بَلَاءٍ حَتَّى يُمْسِيَ»، قَالَ: فَأَصَابَ أَبَانَ بْنَ عُثْمَانَ الْفَالِجُ، فَجَعَلَ الرَّجُلُ الَّذِي سَمِعَ مِنْهُ الْحَدِيثَ يَنْظُرُ إِلَيْهِ، فَقَالَ لَهُ: مَا لَكَ تَنْظُرُ إِلَيَّ؟ فَوَاللَّهِ مَا كَذَبْتُ عَلَى عُثْمَانَ، وَلَا كَذَبَ عُثْمَانُ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَلَكِنَّ الْيَوْمَ الَّذِي أَصَابَنِي فِيهِ مَا أَصَابَنِي غَضِبْتُ فَنَسِيتُ أَنْ أَقُولَهَا.

[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه والنسائي في الكبرى وأحمد] - [سنن أبي داود: 5088]
المزيــد ...

Daga Aban ɗan Usman ya ce: Na ji Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - yana cewa: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Wanda ya ce: Da suna Allah wanda wani abu ba ya cutuwa tare da sunanSa a cikin ƙasa, ko cikin sama, Shi ne Mai yawan ji Masani”. sau uku, wani bala'i na fuj'a ba zai same shi ba har sai ya wayi gari, wanda ya faɗeta lokacin da ya wayi gari sau uku, wani bala'i na fuj'a ba zai same shi ba har sai shiga maraice", ya ce: Sai shanyewar ɓarin jiki ya samu Aban ɗan Usman, sai mutumin da ya ji hadisin daga gare shi ya fara kallonsa, sai ya ce masa: Me yasa meka kake kallona? Na rantse da Allah ban yi wa Usman ƙarya ba, kuma Usman bai yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ƙarya ba, sai dai ranar da abinda ya sameni ya sameni a cikinta na yi fushi sai na manta ban fadi addu'ar.

[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 5088]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya ce da safiyar kowace rana bayan ɓullowar alfijir, da yammacin kowane dare kafin faɗuwar rana sau uku: (Da sunan Allah) ina neman taimako ina neman kiyayewa daga dukkan abinda yake cutarwa (wanda ba ya cutarwa tare da) ambatan (sunanSa), ko (wane abu) duk irin girman da ya yi (a cikin ƙasa) da abinda yake fitowa daga gareta na bala'i (ko a cikin sama) mai saukowa daga gareta na bala'i (Shi Mai yawan ji ne) ga maganganun mu (Masani) da halayenmu.
A Wanda ya faɗeta lokacin da ya shiga maraice bala'i ba zai same shi ba bagtatan har sai ya wayi gari, wanda kuma ya faɗeta lokacin da ya wayi gari bala'i bagtatan ba zai sameshi ba har sai ya shiga maraice.
Sai maruwaicin hadisin Aban ɗan Usman ya samu cutar shanyewar ɓarin jiki; shi ne shanyewar ɓarin jiki, sai mutumin da ya ji hadisin a wunsa ya fara kallon Aban yana mai mamaki! sai mutumin ya ce: Me ya sameka ne kake kallona?! Na rantse da Allah ban yi wa Usman ƙarya ba, kuma Usman bai yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ƙarya ba, saidai a ranar da abin ya sameni a cikinta Allah bai ƙaddara mini faɗinta ba, fushi ne ya sameni sai na manta in faɗi waɗannan kalmomin da aka ambata.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الرومانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so yin wannan zikirin a safe da maraice; dan mutum ya zama abin kiyayewa da izinin Allah - Maɗaukakin sarki - daga wani bala'i na fuj'a ko cuta ta same shi ko makamancin hakan.
  2. Ƙarfin yaƙinin magabata na farko da Allah da kuma gasgatawarsu ga abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari da shi.
  3. Daga fa'idojin ƙayyade zikiri safe da yamma (shi ne) yanke rafkana daga musulmi da halartowarsa a dawwame cewa shi bawan Allah ne - Maɗaukakin sarki -.
  4. A bisa gwargwadan imanin mai ambatan Allah da khushu'insa da halartowar zuciyarsa, tare da ikhlasi da yaƙini gurbin zikirin yake zama abin tabbatarwa.