+ -

عن أبي مسعود رضي الله عنه قال: قال النبي صلى الله عليه وسلم:
«مَنْ قَرَأَ بِالْآيَتَيْنِ مِنْ آخِرِ سُورَةِ الْبَقَرَةِ فِي لَيْلَةٍ كَفَتَاهُ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5009]
المزيــد ...

Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi.

Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin duk wanda ya karanta ayoyi biyun ƙarshe na Suratul Baƙara cikin dare, to, Allah zai tsare shi daga sharri da abin ƙi, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi nafilar dare, wasu kuma suka ce: Sun ishe shi addu’oin dare. An ce kuma: su ne mafi ƙarancin abin da zai isa na karatun Alkur’ani a nafilar dare, an ma faɗi wanin haka, kuma muna fatan duk abin da aka faɗa ɗin daidai ne, domin zai ƙunshe su duka

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية القيرقيزية النيبالية اليوروبا الليتوانية الدرية الصومالية الكينياروندا الرومانية المجرية التشيكية المالاجاشية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin falalar [ayoyin] ƙarshen Baƙara, su ne daga faɗin Allah: (( Manzon ya yi imani….. har zuwa ƙarshen Surah.
  2. Ƙarshen Suratul Baƙara yana tunkuɗewa wanda ya karanta mugun abu da sharri da shaiɗanu, idan ya karanta su da daddare.
  3. Dare yana farawa ne daga faɗuwar rana, yana kuma ƙarewa ne da hudowar alfijir.