عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«مَنْ قَرَأَ حَرْفًا مِنْ كِتَابِ اللهِ فَلَهُ بِهِ حَسَنَةٌ، وَالْحَسَنَةُ بِعَشْرِ أَمْثَالِهَا، لَا أَقُولُ {الم} حَرْفٌ، وَلَكِنْ {أَلِفٌ} حَرْفٌ، وَ{لَامٌ} حَرْفٌ، وَ{مِيمٌ} حَرْفٌ».
[حسن] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 2910]
المزيــد ...
An karbo daga Abdullahi Ɗan Mas’ud Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
"Duk wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah, to, yana da lada, kuma kowane lada za a ninkashi goma. amma ba zan ce Alif Laam Meem harafi ɗaya ba ne, sai dai Alif, harafi ne, Laam harafi ne, Meem harafi ne"
[Hasan ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi] - [سنن الترمذي - 2910]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labari cewa kowanne Musulmi ne ya karanta harafi daga littafin Allah, to, yana da lada a wannan karatun, kuma za a ninka masa lada zuwa ninki goma.
Sannan ya yi bayanin hakan da faɗinsa: Ban ce : Alif, Laam, Meem, harafi ba ne, sai dai Alifun harafi ne, Lamun harafi ne, Mimun harafi ne, sai ya kasance harufa uku, lada talatin kenan.