عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«تَعَاهَدُوا هَذَا الْقُرْآنَ، فَوَالَّذِي نَفْسُ مُحَمَّدٍ بِيَدِهِ لَهُوَ أَشَدُّ تَفَلُّتًا مِنَ الْإِبِلِ فِي عُقُلِهَا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 791]
المزيــد ...
Daga Abu Musa Al-ash'ariy Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
Ku dinga maimaita wannan Alƙur’anin, ina rantse muku da wanda ran Muhammad yake a hannunSa ya fi saurin kufcewa sama da raƙumin da ya ke a dabaibayi.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 791]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarnin yawan maimaita Alƙur’ani da dagewa a kan karanta shi; domin kada a manta bayan an haddace shi a zuciya, [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kuma ƙarfafi hakan da rantsuwa a kan Alƙur’ani ya fi saurin ɓacewa da tafiya daga zuciya a kan raƙumi da aka ɗaure, ga shi a ɗaure da igiya a ƙwauri, idan mutum yana yawan bibiyarsa sai ya riƙeshi, idan kuma ya sakeshi sai ya tafi ya ɓace.