+ -

عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«يقالُ لصاحبِ القرآن: اقرَأ وارتَقِ، ورتِّل كما كُنْتَ ترتِّل في الدُنيا، فإن منزِلَكَ عندَ آخرِ آية تقرؤها».

[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي في الكبرى وأحمد] - [سنن أبي داود: 1464]
المزيــد ...

Daga Abdullahi dan Amr dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Za'a ce da ma'abocin Alkur’ani: Karanta ka daukaka, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya, domin cewa matsayinka zai tasayane a karshen ayar da ka karantata".

[Hasan ne] - - [سنن أبي داود - 1464]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa, za’a ce da makarancin Alkur’ani, mai aiki da abinda ke cikinsa, wanda ya lazimceshi a karatu da hadda idan ya shiga Aljanna: Ka karanta ka daukaka da wannan a cikin darajojin Aljanna, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya da karanta shi da bi ahankali da nutsuwa; domin cewa matsayinka na karshen ayar da ka karantata ne.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy الفولانية Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch اليونانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Sakayya tana daidai da dacewar ayyuka a yawa da yanayi.
  2. Kwadaitarwa akan karatun Alkur’ani da kyautata shi da hardace shi da tadabburi da kuma aiki da shi.
  3. Aljanna masaukaice darajoji masu yawa, ma'abota Alkur’ani zasu samu madaukakan darajoji a cikinta.